Kudin Da Aka Samu Daga Kallon Fina-Finai A Bikin Bazarar 2025 Ya Kafa Tarihi
Published: 2nd, February 2025 GMT
Masana’antar shirya fina-finai ta kasar Sin ta kafa wani sabon tarihi a hutun bikin bazarar 2025, inda daga ranar 29 ga watan Janairu zuwa ranar 1 ga Fabrairu, kudaden da aka samu daga kallon fina-finai ya kai biliyan 5.75 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 802, wanda ya zarce mafi yawan kudin da aka samu a baya na yuan biliyan 5.
73 a shekarar 2021.
Wannan adadi shi ne mafi yawan kudi da aka samu daga kallon fina-finai a lokacin bikin bazara a tarihin sinima ta kasar, kuma ya tabbatar da matsayin kasar Sin na kasancewa jagora wajen samun mafi yawan kudade daga kallon fina-finai wato box office a shekarar 2025, wanda ya zarce Arewacin Amurka.
Gwamna Buni Ya Jaddada Bai Wa Sojoji Gudunmawar Kawo Karshen Boko Haram An Kammala Aikin Tsugunar Da Mutane A Gundumar Tingri Ta Sin Bayan Bala’in Girgizar KasaBisa al’ada bikin bazara kololuwar lokaci ne na zuwa kallon fina-finai da samun riba ga masu shirya fina-finai, an samu zazzafar gasa tsakanin manyan fina-finai da aka saki. An kuma tsawaita hutun bikin bazara da kwana daya zuwa kwanaki takwas a wannan shekara, wanda ke gudana daga ranar 28 ga Janairu zuwa 4 ga Fabrairu.
Carton mai sun “Ne Zha 2” ne ke kan gaba a jerin manyan shirye-shirye, wanda ya samu sama da yuan biliyan 2.3 a cikin kwanaki hudu kacal, a cewar bayanan da kafar Beacon mai bibiyar fina-finan box office ya fitar. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
এছাড়াও পড়ুন:
Ina Fatan Ci Gaba Da Kasancewa A Manchester United – Onana
Tom Heaton da Altay Bayindir ba su samu lokacin da suke bukata a United ba, Bayindir ya buga kananan wasanni a kakar wasa ta bana, amma kuma tsohon mai tsaron ragar na Fenerbahce na fatan ganin ya samu karin lokacin buga wasanni kamar sauran yan wasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp