Ƴansanda Sun Daka Wasoso Kan Gungun Ƴan Daba A Kano
Published: 3rd, February 2025 GMT
Rundunar Ƴansandan jihar Kano ta cafke wasu matasa a yankin Sheka bayan ɓarkewar rikici tsakanin ƙungiyoyin ƴan daba.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook, yana mai cewa rikicin ya fara ne bayan mutuwar wani matashi mai suna Yusuf Aminu, ɗan unguwar Sheka Babban Layi, wanda ake zargi da aikata fashi da sauran laifuka.
Rahotanni sun nuna cewa marigayin mamba ne na ƙungiyar ‘Yan Shida,’ wacce ta addabi yankin Sheka da aikata fashi da tashin hankali. Wasu mazauna unguwar sun kama shi, suka kakkarya masa ƙafa tare da jikkata wasu, wanda hakan ya kai ga mutuwarsa.
Bayan faruwar lamarin, abokan marigayin suka yi ɗamarar ɗaukar fansa, lamarin da ya janyo rikici mai muni a yankin. Sai dai ‘yansanda sun yi gaggawar shiga tsakani, suka kama wasu daga cikin matasan tare da maido da doka da oda a yankin.
এছাড়াও পড়ুন:
Kotu ta tsare ’yan TikTok 2 a Kano
Wata Kotun Majistire mai lamba 7 a Kano, ta bayar da umarnin tsare wasu ’yan TikTok biyu kan zargin wallafa wasu bidiyon batsa a shafukansu na dandalin sada zumunta.
Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano ce ta gurfanar da ababen zargin biyu — Isa Kabir Brigade da Fatima Adam Kurna — kan wallafa bidiyon da suka saɓa wa tarbiyya da addini.
An rantsar da shugabannin ƙananan hukumomi 34 na Katsina ’Yar shekara 66 ta haifi ɗanta na 10 da kantaSai dai bayan lauyan da ke ɓangaren masu shigar da ƙara, Garzali Maigari Bichi ya karanta musu ƙunshin tuhume-tuhumen, sun musanta wasu daga ciki.
Dangane da hakan ne Alƙalin Kotun, Halima Wali ta bayar da umarnin tsare ababen zargin tare da ɗage zaman kotun zuwa ranar 24 ga watan Afrilu.
Ana iya tuna cewa dai Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano ta ɗaura ɗamarar tsaftace dandalan sada zumunta ta hanyar kame da ladabtar da masu wallafe-wallafen duk wani abu da ya ci karo da tarbiyya da addini.
Ko a bayan nan sai da hukumar ta gurfanar da wasu mutum biyu — waɗanda aka yankewa hukuncin ɗauri na shekara guda ko zaɓin biyan tara ta Naira dubu 100 — kan wallafa bidiyon batsa a shafukansu na TikTok.