NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Za Mu Kashe Biliyan N2.5 Kan Auren Zawarawa —Gwamnatin Kano
Published: 3rd, February 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Tun bayan da Gwamnatin Kano ta sanar cewa ta ware Naira biliyan biyu da rabi don aura da ’yan mata da zawarawa a jihar batun ke ta shan suka daga ɓangarori daba-daban.
Wasu na ganin jihar na da wasu buƙatun da suka fi auren gatan muhimmanci da ya kamata gwamnatin ta fi mayar da hankali a kansu.
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana ya yi nazari ne kan dalilan da Gwamnatin Kano ta ware Naira biliyan biyu da rabi don aurar da ’yan mata da zawarawa.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan mata Hukumar Hisbah
এছাড়াও পড়ুন:
Abincin karnuka ya fi namu —Fursunonin Najeriya
Fursunoni a gidajen yarin daban-daban a sassan Najeriya sun koka game da munin irin abincin da ake ba su, wanda suka ce na karnuka ya fi shi.
Da dama daga cikin fursunonin da muka zanta da su sun bayyana cewa takwarorinsu sun sha mutuwa a sakamakon yunwa.
Wannan zargi na zuwa ne bayan da Hukumar Gidajen Yari ta Najeriya tare da wani kwamitin bincike mai zaman kansa sun ƙaryata zarge-zargen fursunonin kan yunwa a gidajen yari.
A watan Satumban 2024 ne Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya kafa a kwamitin domin gudanar da bincike kan zargin jami’an gidajen yari da cin hanci da kuma cin zarafin fursunonin.
NAJERIYA A YAU: Dalilan Farfaɗowar Boko Haram A Jihar Borno An sake kama wasu mafarauta ’yan Kano a Jihar Edo NAJERIYA A YAU: Dalilan Farfaɗowar Boko Haram A Jihar BornoDuk da cewa kwamitin ya tabbatar da zargin yunwa da fursunonin suka yi, Muƙaddashin Shugaban Hukumar Gidajen Yari ta Kasa, ya ce an zuzuta lamarin, saboda a cewarsa, babu alƙaluman da ke tabbatar da hakan.