HausaTv:
2025-04-14@18:03:17 GMT

 An Fito Da Gawawwakin Shahidai Fiye Da 400 Daga Karkashin Baraguzai A Gaza

Published: 3rd, February 2025 GMT

Ma’aikatan Agaji suna ci gaba da fito da gawawwakin shahidan Falasdinawa da Isra’ila ta rushe gidaje akansu, a tsawon lokacin yaki,wasu kuma akan hanyoyi.

Wani jami’in agaji ya ce, bayan gushewar fiye da shekara daya na yaki, da wuya suke iya samun cikakkiyar gawar wani daga cikin shahidai, sai dai  rabi da rabi, a wasu wuraren ma dai sai dai kasusuwa.

Ya zuwa yanzu dai an sami gawawwakin da sun kai 458 kamar kakakin ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu Dr.  Khalil Dakran ya ambata.

Ma’aikatar kiwon lafiyar ta Falasdinawa tana kirdadon cewa za a iya samun gawawwakin da suke tsakanin 4000, zuwa 5000 a karkashin baraguzai a fadin Falasdinu.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Gaza: Mutane 38 Sun Yi Shahada A Yau Litinin

Majiyar asibiti a yankin Gaza, ta ambaci cewa an sami karuwar shahidai a cikin sassa mabanbanta na zirin Gaza zuwa 38, 3 daga cikinsu a yankin Deir-Balah.

Jiragen yakin HKI sun kai wasu hare-hare akan wata mota da take dauke da wasu ‘yan’uwa shakikai su 6, da hakan ya yi sanadiyyar shahadarsu baki daya.

‘Yan’uwan 6 da su ka yi shahadai, suna aiki ne da wata kungiyar agaji da take rabawa ‘yan hijira kayan abinci da sauran na bukatunsu na yau da kullum.

Sojojin HKI sun fitar da wata sanarwa da a ciki su ka riya cewa, wadanda su ka kai wa harin suna Shirin kai musu hari ne.

A jiya Litinin da marece sojojin HKI sun rushe wasu gidaje a yammacin garin Rafah a kudancin zirin Gaza.

A yammacin sansanin ‘yan hijira dake yammacin Khan-Yunus, jirgin sama maras matuki na HKI ya kai hari da hakan ya yi sanadin shahadar mutane biyu,kmar yadda su ka kashe shugaban ‘yan sandan yankin yammacin Khan-Yunus.

Wata sanarwa ta rundunar sojan HKI ta ce, a cikin kwanaki biyu da su ka gabata sun kai hare-hare ta sama har sau 90 a fadin yankin Gaza.

A wani labarin na daban, sojojin HKI sun gargadi mazauna unguwanni daban-daban a kudancin Khan-Yunus da su fice daga cikinsu, saboda za su rusa su. Unguwannin da gargadin ya shafa sun hada Qizan-al-Najjar, Abu Rashwan, Assalam da Manarah. Sai kuma unguwannin Qarin, Ma’an, Batan-al-Yasmin da Fakhari. Haka nan kuma Bani Suhailah ta kudu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Tsoffin Ma’aikatan Hukumar Leken Asiri HKI  Mosad Sun Shiga Cikin Masu Kiran A Kawo Karshen Yaki Da Gaza
  • Gaza: Mutane 38 Sun Yi Shahada A Yau Litinin
  • Al’ummar Mauritaniya Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Nuna Adawa Da Yakin Gaza
  • Bam Ya Halaka Mutum 8, Ya Jikkata Wasu Da Dama A Borno
  •  Nigeria: Wani Bom Da Ya Tashi A Maiduguri Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 7
  • Gaza: Sojojin HKI Sun Sake Kai Wa Asibitin “Ma’amadani Hari
  • Me Ya Janyo Jifan Mawaka A Arewacin Nijeriya?
  • MDD: Mafi Yawancin Wadanda Yaki Ya Ci A Gaza Mata Ne Da Kananan Yara
  • Ficewar Kasar Nijar Daga Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kasa Da Kasa Barazana Ce Ga Tsaro -Hedikwatar Tsaro
  • Sin Za Ta Kara Harajin Fito Kan Hajojin Amurka Da Ake Shigarwa Kasar Zuwa 125%