Abdumalik Alhusi Ya Ce, A shirye Suke Su Koma Yaki Idan HKI Ta Ci Gaba Da Keta Wutar Yaki
Published: 3rd, February 2025 GMT
Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Sayyid Abdulmalik al-Husi ya yaba wa yadda kungiyar Hamas ta jajurce da ci gaba da wanzuwa a dunkunle duk da cewa kwamandan dakarunta Muhamamd Dhaif ya yi shahada.
Jagoran kungiyar ta Ansarullah ya gabatar da jawabi ne na tunawa da zagayowar lokacin shahadar Salih al-Simad wanda daya ne daga cikin manyan shugabannin Ansarullah, ya kara da cewa, ci gaba da wanzuwar kungiyar ta Hamas yana daga cikin muhimman ayyukan da Muhammad Dhaif ya aiwatar a lokacin rayuwarsa.
Sayyid Abdulmalik al-Husi ya mika sakon ta’aziyyar shahadar Muhammad Dhaif ga kungiyar ta Hamas, tare da bayyana shi a matsayin daya daga cikin manyan jagorori abin koyi saboda ruhinsa na imani mai karfi, azama da ruhi na jihadi.
Da yake Magana akan yadda al’ummar Yemen su ka taimakawa gwgawarmayar Falasadinawa, Sayyid Abdulmalik al-Husi, ya kara da cewa; Idan har ‘yan sahayoniya su ka koma yaki, to su ma mutanen Yemen za su koma fagen dagar taimakawa Falasdinawa.
Dangane da kasar Lebanon ma Sayyid Abdulmalik al-Husi ya yi yabo akan yadda al’ummar kudancin kasar suka koma garuruwansu da hakan yake a matsayin babban jihadi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Matasa Sun Daka Wawasu Kan Tirelar Kayan Agajin Ramadan Na Seyi Tinubu A Gombe
Shirin ya fuskanci suka sosai a shafukan sada zumunta, inda suke ganin cewa, Arewa ta cancanci kulawa fiye da haka, yayin da wasu kuma ke ganin tallafin ya dace.
A wani faifan bidiyo da Daily Trust ta gani, an ga wasu fusatattun matasa suna kwashe kayan abinci a wata babbar mota da aka ajiye a bakin titi.
An ga matasan suna jefo kayan ga wadanda suke kasa domin tattarawa musu, sannan suka yi awon gaba da kayayyakin.
Abubuwan da ke cikin Tirelar sun haɗa da shinkafa, sukari, man girki, gishiri da taliya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp