Bbaban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya Lahadi ya bayyana cewa; Za a yi jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah tare da Shahid Sayyid Hashim Safiyuddin.

Sheikh Na’im Kassim ya kara da cewa, za a binne Shahid Sayyid Hassan Nasrallah a wani wuri dake kusa ba filin saukar jiragen sama na birnin Beirut, yayin da shi kuma Sayyid  Hashim Safiyuddin za a binne shi a mahaifarsa ta Deir-Kanun dake kudnacin Lebanon.

Wani bayanin da Sheikh Na’im Kassim ya yi, shi ne cewa bayan shahadar Sayyid Hassan Nasrallah an zabi Sayyid Safiyuddin Hashim, saidai gabanin su sanar da kwanaki shi ma ya yi shahada.

Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya ce, taken da za a daga a yayin jana’izar shi ne; “Muna Nan A Kan Riko Da Alkawali.”

 A gefe daya, Sheikh Na’im Kassim ya yi Magana akan yadda sojojin HKI suke ci gaba da keta tsagaita wutar yaki, tare da yin kira ga mahukuntan kasar da su dauki matakan da su ka dace.

Haka nan kuma babban sakataren kungiyar ta Hizbullah ya jinjinawa jaruntar mutanen kudancin Lebanon da su ka kutsa cikin garuruwansu duk da cewa, sojojin HKI suna ciki, domin isa gidajensu.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Shahid Sayyid

এছাড়াও পড়ুন:

Babban Kusa A Kungiyar Hamas Salah Al-Bardawil Ya Yi Shahada

Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta fitar da wata sanarwa dangane da shahadar Salah al-Bardawil, mamba a ofishin siyasa na kungiyar kuma wakilin majalisar dokokin Falasdinu.

A rahoton tashar Al-Alam, bayanin Hamas yana cewa: Dr. Salah Al-Bardawil, wanda ya yi fice a fagen siyasa, kafofin watsa labarai, da fagage na kasa da kasa, kuma ake kallonsa a matsayin daya daga cikin manyan kusoshin Hamas, wanda yake a kan gaba wajen gwagwarmaya da  sadaukarwa, ya yi shahada a kan tafarkin gaskiya.

Bayanin ya ci gaba da cewa: Bai taba gazawa wajen gudanar da ayyukansa na jihadi da hidima ga al’ummar Palastinu ba, ya kuma ci gaba da yin gwagwarmaya kan turba ta gaskiya da neman ‘yanci har zuwa karshen rayuwarsa.

Hamas ta jaddada cewa,  jinin Dakta Al-Bardawil da matarsa ​​da sauran shahidai wata fitila ce da za ta haskaka hanyar samun ‘yanci ga al’ummar Falastinu, kuma laifuffukan makiya ba za su taba raunana azama da jajircewar ‘yan gwagwarmaya a Falastinu ba.

A karshen wannan sanarwa da ta fitar a wannan Lahadi 23 ga Maris, 2025, kungiyar Hamas ta yi fatan samun rahama da aljannah ga Dr. Salah Bardawil da matarsa, tare da sauran wadanda suka yi shahada a kan tafarkin gaskiya.

Salah Al-Bardawil da matarsa ​​sun yi shahada ne a daren ranar 23 ga watan Ramadan, bayan wani hari da yahudawan sahyuniya suka kai a kan tantin su da suke a  yankin Al-Mawasi da ke yammacin birnin Khan Yunus.

Wannan harin dai wani bangare ne na kisan gilla da yahudawan Haramtacciyar Kasar Isra’ila  suke ci gaba da yi kan al’ummar Gaza marasa kariya, tare da samun cikakken goyon baya da karfin gwiwa da dukkanin taimako kan hakan daga gwamnatin kasar Amurka.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • NUJ Ta Bada Tallafin Azumi Ga Iyalan Mambobinta Da Suka Rasu A Jihar Kebbi
  • SDP: Ba Mu Yi Wa Kowa Alƙawarin Takarar Shugaban Ƙasa Ba
  • Mutum 2,000 za su riƙa kamuwa da cutar HIV duk rana a duniya — MDD
  • ‘Yansanda Sun Cafke Mutum 2 Kan Zargin Kashe Ɗan Achaɓa Da Sace Babur Ɗinsa A Bauchi 
  • Babban Kusa A Kungiyar Hamas Salah Al-Bardawil Ya Yi Shahada
  • Al-Huthi Ya Ce Kawo Wani Jirgin Ruwa Mai Daukar Jiragen Saman Yaki Gazawa Ce Ga Amurka
  • Gombe Za Ta Kashe Naira Biliyan 1.1 Don Samar Da Fitilun Hanya Masu Aiki Da Hasken Rana
  • Dole Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Ta Daina Barazana Ga Masu Sukar Ta – Amnesty
  • Moscow : Dole ne Rasha da China su shiga tattaunawar nukiliya da Iran
  • Ko Raunin ‘Yan Wasa Zai Rage Wa Barcelona Karsashi A Kakar Bana?