Jakadiyar MDD na musamman kan al-amuran Falasdinawa, ta bada sanarwan cewa HKI ta fadada aikin kissan kare dangi da take yi a Gaza zuwa dukkan kasar Falisdinu, ta kuma kara da cewa wannan halin ya nuna cewa HKI tana son ta kara fadada kissan kiyashin zuwa garin Jenin da kuma yankin yamma da kogin Jordan gaba daya.

Francesca Albanese ta bayyana haka ne a shafin ta na X, a jiya Lahadi, ta kuma yi kira ga kasashen duniya su shigo cikin al-amarin don kawo karshen kisan kare dangi da kuma rusa gidajen Falasdiwa da ta fara a yankin Jeneen. Daga karshe Jami’ar ta MDD ta bayyana cewa a halin yanzu kissan kiyashi da rushe-rudhen gidajen falasdinawa bai tsaya kan Gaza kadai ba, amma ya hada da yankin yamma da kogin Jordan da aka mamaye.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Ce Kasar Wacce Ta Fi Shigar Da Kayakin Kasuwanci Zuwa Kasar Afganistan A Shekarar Da Ta Gabata

Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Afganistan ta bada sanarwan cewa kasar Iran ce a gaba da dukkan kasashen makobta da kasar Afganisatan wacce tafi shigo da kayakinta cikin kasar a shekara ta 1403 ta kalandar Iraniyawa da ta kare.

Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar kasuwanci ta kasar Afganistan Abdussalam Jawad Okhande-Zadeh ya na fadar haka a yau Lahadi:

Ya kuma kara da cewa, kasashen da suka shigo da kayaki a kasar Afganistan a shekarar da ta gabata sun hada ta Iran, a gaba da ko wace kasa, sannan Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Pakisatn, China da kuma Turkamanistan.

Kakakin ma’aikatar kasuwancin ta kasar Afganisatn ya ce a dayan bangaren kuma kasar Afaganista ta fidda kayaki zuwa kasashen waje wadanda kimarsu ya kai dalar Amurka biliyon guda a shekarar da ta gabata, kuma sun hada da busassun yayan itace, da darduma, da awduga da duwatsu masu daraja.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Ce Kasar Wacce Ta Fi Shigar Da Kayakin Kasuwanci Zuwa Kasar Afganistan A Shekarar Da Ta Gabata
  • Hukumar Birnin Istambul Ta Dakatar Da Akram Imamoglu Daga Matsayinsa Na Magajin Garin Birnin
  • Yadda garin Zip ya nutse a Kogin Binuwai
  • Fadin Yankin Da Ke Fama Da Zaizayar Kasa Na Kasar Sin Ya Ragu A 2024 
  • An gudanar da gagarumar zanga-zangar nuna goyon bayan Falastinu a kasar Jordan
  • Iran da UAE sun kirayi Isra’ila da Amurka da su kawo karshen hare-harensu a Gaza da Yemen
  • A cikin kwanaki 3 Falasdinawa 605 sun yi shahada a kisan kiyashin Isra’ila a Gaza
  • Cibiya Mai Fafutukar Kare Hakkokin Falasdinawa “Global 195” Ta Shelanta Farautar Sojojin HKI Da Su KaTafka Laifukan Yaki
  • Gwamnoni Na Kamun Kafa A Wurin Tinubu Don Hana Bai Wa Kananan Hukumomi ‘Yanci
  • Araghchi : Iran za ta mayar da amsa ga wasikar Trump cikin kwanaki masu zuwa