Zazzabin Lassa ya kashe mutum biyu a Filato
Published: 3rd, February 2025 GMT
Mutum biyu sun rasu sakamakon bullar cutar zazzabin Lassa a Jihar Filato.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Filato, Dakta Cletus Shurkuk, ya sanar cewa mutum na uku da ya kamu da cutar yana samun kulawa a asibiti.
Ya bayyana cewa mamatan sun kamu da cutar ne a Karamar Hukumar Kanam, na ukun da ke raye kuma a Karamar Hukumar Shendam.
Daya daga cikin majinyatan ya rasu ne a Shendam na biyun kuma a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.
Gwamnatin Najeriya za ta sake ƙara kuɗin lantarki NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Za Mu Kashe Biliyan N2.5 Kan Auren Zawarawa —Gwamnatin KanoKwamishinan ya bayyana cewa gwamanatin jihar tana aiki tare da Cibiyar Yaki da Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) domin dakile yaduwar cutar.
Ya ce tun da suka samu rahoton bullar cutar suka tura jami’ansu zuwa yankunan domin yin gwaji ga wadanda suka yi mu’amala da marasa lafiyan da kuma wayar da kan jama’a kan hanyoyin kariyar cutar.
Ya shawarci al’ummar jihar da su kasance masu kula da tsaftar muhalli domin dakile yaduwar cutar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Hajjin 2025: Shirye-shirye Sun Yi Nisa A Jihar Jigawa
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce shirye-shirye sun yi nisa game da aikin Hajjin shekarar 2025 a jihar.
Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ne ya bayyana hakan ga Radio Nigeria a hedikwatar hukumar da ke Dutse.
A cewarsa, zuwa yanzu hukumar ta mika sunayen maniyyata fiye da dubu ɗaya da suka kammala biyan kuɗin aikin Hajji daga jihar zuwa ga Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON).
Ya ce tuni aka fara shigar da waɗanda suka kammala biyan kuɗin cikin tsarin neman biza.
Labbo ya bayyana cewa hukumar ta biya Hukumar Hajji ta Ƙasa kuɗi naira biliyan takwas a madadin alhazan jihar na shekarar 2025.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce ana gudanar da tarukan bita ga maniyyata a kullum, a kananan hukumomi 27 na jihar, ta hannun wasu malamai don ilmantar da su game da aikin hajjin.
Ya ƙara da cewa hukumar za ta raba jakunkuna da za su daukin nauyin kilo 8 da unifom ga jami’an yankuna da cibiyoyi domin rabawa mahajjatan.
Shugaban hukumar ya ja hankalin maniyyatan da su riƙa halartar traon bita saboda muhimmancinsa.
Ya yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa goyon baya da haɗin kai da yake ba hukumar domin samun nasarar gudanar da aikin hajji ba tare da wata tangarda ba.
Radio Nigeria ta ruwaito cewa Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta ware kujeru sama da 1,800 ga jihar domin aikin hajjin bana.
Usman Muhammad Zaria