Aminiya:
2025-03-25@18:00:30 GMT

Alawar yara mai sanya maye ta shiga gari —NDLEA

Published: 3rd, February 2025 GMT

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) a Jihar Kano ta gargaɗi al’umma kan wata alawar yara mai da sanya maye, da ke yawo a gari.

Hukumar ta gargaɗi, musamman iyaye da su yi hattara da alawar da sauran kayan tanɗe-tanɗe da ke ɗauke da sinadarai masu sanya maye.

Kakakin Hukumar a jihar, ASN Sadiq Muhammad Maigatari, ya kuma yi kira ga iyaye da suka riƙa lura da irin kayan tanɗe-tanɗe da ’ya’yansu ke saya.

Ya bayyana cewa alawar tana kama da cakulet, amma a cikinta an sanya abin da ke bugarwa, kuma yawanci an fi sayarwa a makarantu.

NHIS: Kotu ta tsare Farfesa Usman Yusuf a Gidan Yarin Kuje Gwamnatin Najeriya za ta sake ƙara kuɗin lantarki NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Za Mu Kashe Biliyan N2.5 Kan Auren Zawarawa —Gwamnatin Kano

Don haka ya buƙaci iyaye da su riƙa sanya ido, musamman idan suka ga wani sauyi a yanayin ’ya’yan nasu.

Ya ce, “sauyin ya haɗa da na yanayin cin abinci da na barcin yara.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: alawa alawa mai sanya maye

এছাড়াও পড়ুন:

INEC Ta Karɓi Takardun Yi Wa Sanata Natasha Akpoti Kiranye 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gaskiyar abin da ake faɗa kan ’yan fim — Samira Sani
  • INEC Ta Karɓi Takardun Yi Wa Sanata Natasha Akpoti Kiranye 
  • NDLEA Ta Kama Ƴar Indiya Ɗauke Da Hodar Iblis A Kano
  • UNICEF: Yara a Gaza suna fama da matsalar kwakwalwa da ba a taba ganin irinsa ba
  • Hukumar Birnin Istambul Ta Dakatar Da Akram Imamoglu Daga Matsayinsa Na Magajin Garin Birnin
  • Bututun Iskar Gas Ya Sake Fashewa A Ribas
  • An shiga ruɗani yayin da Sanusi II da Bayero ke shirin hawan salla a Kano
  • An Kashe Askarawa 6 da ‘Yan Sa-kai 4 A Zamfara 
  • Gwamnatin Kano Ga Ma’aikata: Duk Mai Bukatar Aikinsa Dole Ya Gabatar Da Kansa A Wajen Tantancewa
  • Isra’ila : ‘Yan adawa sun kira zanga-zangar gama-gari bayan korar shugaban Shin Bet