Uwargidan Gwamnan Jigawa Ta
Published: 3rd, February 2025 GMT
Uwargidan Gwamnan Jihar Jigawa, Hajiya Hadiza Umar Namadi ta kaddamar da wani katafaren wurin shan shayi da taliya na zamani a karamar hukumar Maigatari ta jihar.
Hajiya Hadiza Namadi ta ce, wurin sayar da shayin da taliyar da aka zamanantar da shi wani yunkuri ne na karamar hukumar ta Maigatari.
Ta kara da cewa, an tsara wannan wurin na zamani ne domin samar da yanayi mai kyau da inganci ga mutane, inda za su ci abinci cikin gamsuwa, tare da bunkasa kasuwanci a yankin.
Hajiya Hadiza ta kuma kaddamar wani tallafi ga mata 300 a karamar hukumar Maigatari.
An bayar da naira dubu talatin kowannensu, domin bunkasa kananan sana’o’i.
Gidan rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, a yayin bikin, uwargidan gwamnan, Hajiya Hadiza Umar Namadi ta gabatar da takardun kama aiki na wucin gadi ga malaman makaranta su 173.
A zantawar wakilinmu da wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin, sun yabawa shugaban karamar hukumar Maigatari bisa wannan karimcin.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa Karamar hukumar Maigatari karamar hukumar Hajiya Hadiza
এছাড়াও পড়ুন:
CMG Ya Kaddamar Da Nuna Fina-Finai Da Shirye-Shiryen Talabijin Na Kasar Sin Masu Inganci A Malaysia
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp