Hukumar sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta kasa NDLEA ta ce an yi wa wani mutum mai shekara 59 tiyata domin ciro sunƙin hodar ibilis 57 cikin guda 81 da ya haɗiye kwanaki bakwai da suka gabata a Addis Ababa da ke kasar Habasha.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya fitar, ta ce an kama mutumin ne a lokacin da ake tantance fasinjoji bayan isar su filin jirgin sama na Murtala Muhammad daga Habasha a ranar 26 ga watan da ya gabata.

Kakakin hukumar ya ce bincike ya gano cewa mutumin wanda ya yi iƙirarin ɗan kasuwa ne a yankin Oshodi da ke jihar Lagos, ya tafi Addis Ababa inda ya haɗiyi sunƙi 81 na hodar ibilis ɗin, daga bisani kuma ya hau jirgi zuwa Beirut da ke kasar Lebanon domin kaiwa a kan kuɗi dala 3000.

Ya kuma ce binciken nasu ya nuna cewa mutumin bai samu shiga ƙasar ba saboda kuɗin hannunsa ba su kai dala 2,000 ba da ake buƙata kafin shiga ƙasar ta Lebanon, wanda ya sa aka mayar da shi Addis Ababa inda ya yi yunƙirin fitar da miyagun ƙwayoyin amma ya kasa, daga nan kuma ya dawo Najeriya inda suka yi nasarar cafke shi.

Femi ya ƙara da cewa bayan kwanaki 5 ƙarƙashin sa idon hukumar a asibitin koyarwa na Jami’ar Jihar Lagos, mutumin ya yi kashin sunƙin hodar ibilis guda 24, inda daga bisani saboda gujewa kamuwa da rashin lafiya, aka yi masa tiyata domin cire sunƙi 57 da suka rage bayan uwargidansa da ɗan’uwansa sun amince da yin hakan.

bbc

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Hodar Iblis

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 10, sun jikkata 14 a Zamfara

Aƙalla jami’an rundunar tsaron al’umma ta Zamfara (CPG) 10 ne, suka rasu, yayin da wasu 14 suka jikkata a wani hari da ’yan bindiga suka kai musu a yankin Anka da ke Jihar Zamfara.

Sun kai harin ne a ranar Asabar bayan da jami’an tsaro suka kai farmaki wani sansanin ’yan bindiga da ke dajin Bagega a ranar Juma’a da Asabar.

An shiga ruɗani yayin da Sanusi II da Bayero ke shirin hawan salla a Kano Ɗan sa-kai ya kashe matasa biyu a Borno

A yayin farmakin, sun kashe ’yan bindiga da dama kuma sun kuɓutar da wasu mutanen da aka sace a sansanin wani ƙasurgumin shugaban ’yan bindiga, Alhaji Beti.

Wata majiya ta bayyana cewa jami’an tsaro sun kuma ƙone gidan wani shugaban ’yan bindigar mai suna Bellon Kaura, wanda lamarin da ya fusata su.

“Kurakuran da suka yi shi ne komawa ta hanyar da suka bi a lokacin farmakin farko,” in ji wani shugaba a yankin Anka.

“’Yan bindigar sun tsere daga sansaninsu amma sun shirya tarko, sun yi kwanton-ɓauna, kuma suka buɗe wuta bayan jin ƙarar baburan jami’an tsaron.”

Harin ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaro bakwai daga Anka da kuma uku daga Talata Mafara.

Sunayen waɗanda suka rasu sun haɗa da Shehu Lawali, Murtala Mesin, Ubandawaki Moda, Muhammad Want, Haruna Kwanar Maje, Ibrahim Ware Ware, Yusuf Ware Ware, Rabi’u Barbara, Lawali Dan Hassi Jangebe, da Badamasi Gima.

An yi jana’izarsu a Anka a ranar Lahadi, inda Gwamna Dauda Lawal ya halarta, tare da ɗaukar alƙawarin ci gaba da goyon baya wajen yaƙi da ’yan bindiga a jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [17]
  • NDLEA Ta Kama Ƴar Indiya Ɗauke Da Hodar Iblis A Kano
  • Ɗansanda Ya Kashe Matar Abokin Aikinsa, Ya Jikata Wasu Biyu A Ribas
  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [16]
  • Hukumar Birnin Istambul Ta Dakatar Da Akram Imamoglu Daga Matsayinsa Na Magajin Garin Birnin
  • ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 10, sun jikkata 14 a Zamfara
  • Matasa sun kashe yaron da suka yi garkuwa da shi a Bauchi
  • Mutumin da girgizar ƙasa ta razana ya shekara 2 yana zaune a cikin kogo
  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [15]
  • Kao Kim Hourn: Ba Ta Hanyar ‘Siddabaru’ Kasar Sin Ta Cimma Nasarori A Fannin Ci Gaba Ba Sai Dai Ta Hanyar Aiki Tukuru Kuma Mai Dorewa