Masarautar Fika ta buɗe gasar ƙwallon ƙafa karo na uku a Potiskum
Published: 3rd, February 2025 GMT
Masarautar Fika da ke Jihar Yobe ta buɗe gasar ƙwallon ƙafa karo na uku a filin wasa na Dabo Aliyu da ke garin Potiskum.
An buɗe gasar ƙarƙashin jagorancin mai Martaba Sarkin Fika, Alhaji Dr. Muhammad Ibn Abali Muhammad Idris wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Yobe.
Ya je Maiduguri daga Legas a kan keke Rikicin rusau ya yi ajalin mutum 4 a KanoGasar wacce aka fara a shekarar 2011 ta bunƙasa zuwa wani gagarumin taron wasanni a yankin, wadda ke haɗa ƙungiyoyi daga ƙananan hukumomi huɗu na yankin da suka haɗa da Fune, Potiskum, Fika, da Nangere.
A shekarar 2017 aka gudanar da gasar karo na biyu, lamarin da ya ƙara tabbatar da gasar a matsayin ɗaya daga cikin manyan wasannin ƙwallon kafa a jihar.
A wannan shekarar ta 2025 an buɗe gasar ce da wasa tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Total Pillars FC Potiskum da Parma FC ita ma a garin na Potiskum.
Ƙungiyoyin biyu dai sun ƙare zagayen farko ba tare da an zura ƙwallo a raga ba, amma ana minti 19 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Abdulzabi na Parma ya zura ƙwallo daya tilo da aka tashi a wasan, inda ƙungiyar tasa ta samu nasara da ci 1-0.
Gasar ta bana ta samu halartar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa 64 daga ƙananan hukumomi huɗu da suka shiga gasar.
Wani muhimmin abin da ya fi ɗaukar hankali a bikin buɗe gasar shi ne bayar da lambobin yabo ga fitattun mutane domin nuna irin gudunmawar da suke bayarwa wajen wasanni da ci gaban al’ummar wannan masarauta ta Fika.
Waɗanda aka karrama sun haɗa da Alhaji Garba Mohammed, FIFA Lamido, Aliyu Abba Bulama (AFCON), Sadik Rabiu Alkali da Alhaji Ba’aba Abba (Aljino na Fika).
Ana sa ran za a ci gaba da gudanar da gasar nan da makonni masu zuwa, inda za a haɗa haziƙan ’yan ƙwallon ƙafa da masu sha’awar ƙwallon ƙafa daga sassan yankin na Masarautar ta Fika.
Mai Martaba Sarkin Fika, Alhaji Muhammad Ibn Abali Muhammad Idris ya yi fatan alheri ga waɗanda suka samu damar shiga wannan gasa tare da yi musu addu’ar kammala gasar lafiya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Yobe Masarautar Fika ƙwallon ƙafa buɗe gasar
এছাড়াও পড়ুন:
Ana barazanar korar sojojin Isra’ila da ke neman a kawo ƙarshen yaƙin Gaza
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya yi barazanar korar sojojin da ke neman kawo karshen yakin Gaza bayan sun rattaba hannu kan wasu takardu da ke nuna bukatar hakan.
A bayan nan dai fiye da sojoji 1,500 na rundunar da ke kula da tankokin yaƙi ta Isra’ila, ciki har da janar-janar, suka sanya hannu kan wata takardar neman gwamnatin Isra’ila ta mayar da hankali kan dawo da waɗanda aka yi garkuwa da su a Gaza, ko da hakan zai kai ga dakatar da yaƙin da ake yi a yankin Falasdinawa.
Budurwar da ke rayuwa a banɗaki don gudun biyan kuɗin hayar gida HOTUNA: Zulum ya karɓi baƙuncin Majalisar Sarakunan Arewa a BornoA cewar Jaridar Maariv a ranar Litinin, sojoji 1,525 daga rundunar tankokin sun sanya hannu kan wannan takardar, daga masu ɗauke bindiga har zuwa janar-janar.
Sun bukaci gwamnati “ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da an sako wadanda aka yi garkuwa da su — ko da hakan zai kai ga dakatar da yakin.”
Waɗanda suka sanya hannun sun hada da sojojin da suka yi aiki a rundunar kula da tankoki sannan suka koma rayuwar farar hula ba tare da zuwa makarantar jami’ai ba da tsofaffin sojoji da ƙananan kwamandoji, da kuma tsofaffin manyan jami’an sojin Isra’ila, ciki har da tsoffin shugabannin rundunar tankoki da kwamandojin sassa, kamar yadda Maariv ta bayyana.
Sunayen masu sanya hannu sun hada da tsohon Firaminista kuma tsohon shugaban sojoji Ehud Barak da tsohon shugaban rundunar tsakiya Amram Mitzna da tsohon shugaban hafsoshin tsaro Dan Halutz da tsohon shugaban leƙen asiri na soja Amos Malka da tsohon shugaban rundunar tsakiya Avi Mizrahi, da kuma tsohon kwamandan rundunar tankoki ta 14 Amnon Reshef.
Wannan takardar buƙatar ta kasance wani bangare na wani babban kira daga sojoji na yanzu da tsoffin sojojin Isra’ila da ke neman a dawo da wadanda aka yi garkuwa da su tare da kawo karshen yakin.
Tun daga ranar Alhamis, an fitar da kusan takardu goma daga sojoji da ke neman a kawo karshen yakin Gaza.