Aminiya:
2025-03-25@19:46:22 GMT

EU ta yaba wa Gwamna Zulum kan farfaɗo da Jihar Borno

Published: 3rd, February 2025 GMT

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta yaba wa ƙoƙarin Gwamna Babagana Umara Zulum wajen farfado da harkokin rayuwar al’ummar Jihar Borno bayan tashe-tashen hankulan ’yan ta’adda da jihar ta yi fama da shi.

EU ta buga misali da cibiyar koyar da sana’o’i ta Muna da ke horar da matasa musamman waɗanda rikicin Boko Haram ya shafa na tsawon fiye da shekaru goma.

Ya je Maiduguri daga Legas a kan keke Rikicin rusau ya yi ajalin mutum 4 a Kano

Shugaban tawagar Tarayyar Turai a Borno, Ambasada Gautier Mignot ne ya yi wannan yabon a Maiduguri a lokacin da yake zantawa da manema labarai a cibiyar koyar da sana’o’i ta Muna.

Ambasada Mignot ya ce tawagarsa ta yi matuƙar farin ciki da ganin irin damar da cibiyar sana’ar ta ke ba wa al’ummar jihar Borno da ma sauran su.

Ya ce, “Ina yabawa da wannan gagarumin nasara misali ɗaya ne na cibiyoyi da dama da gwamnatin jihar ta gina a ƙarƙashin jagorancin gwamna Zulum da hangen nesansa.

“Koyar da sana’o’i a bayyane yake – abu ne da matasa a jihar ke buƙata, kuma wannan wani abu ne da muka samu a Turai, musamman a Jamus.

“Mun yi nazari kan tarin ayyukan da taimakon jin kai da haɓaka haɗin gwiwa a fannoni da dama da Gwamnan ya aiwatar a Jihar Borno.

“Jihar Borno za ta kasance wani muhimmin yanki na haɗin gwiwar Turai a cikin shekaru masu zuwa.

Wakilin Jakadan Jamus, Karen Jensen, ya yaba wa Gwamna Zulum bisa yadda ya bai wa mata dama ta kowace fuska na rayuwa.

Jensen ya bayyana jin daɗinsa game da yawan mata da ke halartar shirye-shiryen koyar da sana’o’i daban-daban a cibiyar, musamman a fannonin da maza suka fi rinjaye kamar walda, tana mai cewa, “yana da muhimmanci mata su kasance sun samu ilimin sana’a.

“Ina alfahari da abin da nake gani a nan kuma aikin haɗin gwiwarmu yana da kyau sosai,” in ji Jensen.

Aminiya ta ruwaito cewa, tawagar ta je gidan gwamnati ne domin kai wa Gwamna Babagana Umara Zulum ziyara, inda Ƙungiyar Tarayyar Turai ta jaddada ƙudirinta na haɗa gwiwa da Gwamnatin Borno a ayyukan samar da zaman lafiya da hukumar haɗin kan kasa da kasa ta Jamus za ta aiwatar.

Da yake jawabi a wurin taron da ya gudana a Fadar Gwamnatin Borno, wakilin Hukumar Abinci da Aikin Noma na Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO) a Nijeriya da ECOWAS, Koffy Dominique Kouacou, ya yaba da salon jagorancin Gwamna Zulum wajen bunƙasa noma da ƙarfafa tattalin arzikin cikin gida ta hanyar kirkire-kirkire, samar da ababen more rayuwa da sauransu.

Ya ce za su yi aiki tare da Gwamnatin Zulum wajen gano hanyoyin da suka fi dacewa domin tallafa wa ƙoƙarin gwamnatin jihar ta hanyar inganta ayyukan noma, samar da tsarin abinci mai ɗorewa, da baiwa manoma da al’umma damar dogaro da kai.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: jihar Borno Gwamna Zulum jihar Borno Jihar Borno

এছাড়াও পড়ুন:

Fursunoni 12 Sun Tsere Daga Gidan Yari A Jihar Kogi

Gwamnatin jihar ta yi kira ga al’umma da su ba da hadin kai ga jami’an tsaro ta hanyar bayar da bayanai da za su taimaka wajen kamo sauran fursunonin da suka tsere.

Haka kuma, an buƙaci dangin waɗanda suka tsere da su mika kansu ga hukuma domin guje wa hukunci mai tsanani.

Wannan ba shi ne karo na farko da ake samun irin wannan matsala ba, domin a baya an samu fursunoni sun tsere daga gidajen yari daban-daban a Nijeriya.

Hakan na nuni da buƙatar ƙara tsaurara matakan tsaro a gidajen gyaran hali domin hana faruwar irin haka a gaba.

A halin yanzu, jami’an tsaro na ci gaba da bincike tare da ƙoƙarin kamo sauran fursunonin da suka tsere domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kantoman Ribas ya naɗa sabon Sakataren Gwamnati
  • NUJ Ta Bada Tallafin Azumi Ga Iyalan Mambobinta Da Suka Rasu A Jihar Kebbi
  • Fursunoni 12 Sun Tsere Daga Gidan Yari A Jihar Kogi
  • ‘Yansanda Sun Cafke Mutum 2 Kan Zargin Kashe Ɗan Achaɓa Da Sace Babur Ɗinsa A Bauchi 
  • Gwamna Uba Sani Ya Nada Sarkin Kauru Amirul Hajj Na Shekarar 2025
  • Za mu farfaɗo da Madatsar Ruwa ta Biu — Zulum
  • Wasu manyan ’yan Nijeriya sun yi wa Gwamna Radda ta’aziyya a Saudiyya
  • Gobara ta tashi a gidan mai sakamakon fashewar tanka a Neja
  • Gwamnatin Jigawa Ta Nanata Dokar Haramta Kiwon Dare
  • Hikimar Gwamnatin Jihar Jigawa Na Kaddamar Da Shirin Gina Rijiyoyin Burtsatsan Noman Rani