NCDC ta tsaurara matakan shige da fice a Nijeriya saboda fargabar Ebola
Published: 3rd, February 2025 GMT
Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa a Nijeriya (NCDC) ta tsaurara matakan sanya idanu akan hanyoyin shigowa ƙasar sakamakon sabuwar ɓarkewar cutar Ebola a Uganda.
NCDC ta gargaɗi ’yan ƙasar da su guji yin tafiye-tafiye zuwa Uganda saboda ɓullar cutar Ebola da aka tabbatar a ƙasar.
EU ta yaba wa Gwamna Zulum kan farfaɗo da Jihar Borno Masarautar Fika ta buɗe gasar ƙwallon ƙafa karo na uku a PotiskumShawarar NCDC na zuwa ne bayan sanarwar Ma’aikatar Lafiya ta Uganda a ranar 30 ga watan Janairun 2025 kan ɓarkewar wani nau’in cutar Ebola mai suna Sudan a gundumomin Wakiso da Mukono da kuma Mbale na ƙasar.
Ko da yake sanarwar NCDC ta ce ba a samu wani rahoto ba game da ɓullar cutar a Nijeriya, sai dai tun da fari dai Hukumar Lafiya ta Uganda ta ce cutar ta yi sanadiyar mutuwar wani mutum ɗaya kana ana kan bincike wasu 44 a ake zargin ya yi mu’amala da su kai-tsaye.
Sakamakon hakan, NCDC a cikin shawarwarin da ta fitar ta ce duk da cewar babu cutar a Nijeriya, amma tana aiki ne domin daƙile shigowarta.
“NCDC tana koƙari wajen sa ido a wuraren shige da fice a Nijeriya tare da sabunta tsare-tsaren bayar da agajin gaggawa da kuma hanyoyin bincike don gano cutar a manyan ɗakunan gwaje-gwaje da ake da su a manyan biranen da ke da filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa,” a cewar sanarwar gargaɗin da NCDC ta fitar wadda ke ɗauke da sa hannu Darakta Janar Jide Idris.
Haka kuma sanarwar ta ce “duk da cewa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ba ta ayyana dokar hana tafiye-tafiye zuwa Uganda ba, ana gargaɗin duk wanda ya fito daga wuraren da aka samu ɓullar cutar a cikin kwanaki 21 da suka wuce, kuma yake nuna wasu alamomi kamar zazzaɓi da ciwon gabobi da makogwaro da amai da gudawa ko ciwon ciki da dai sauransu, ya gaggauta tuntuɓar Hukumar lafiya ta jihar da yake.”
Kazalika NCDC ta buƙaci ‘yan Nijeriya da su tabbatar an yi musu allurar riga-kafin wasu nau’in cutar Ebola duk kuwa da cewa a yanzu ƙasar ba ta da na nau’in cutar na Sudan da ya ɓarke a Uganda.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Iyakokin Nijeriya cutar Ebola
এছাড়াও পড়ুন:
An naɗa mace ta farko mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya
An naɗa mace ta farko a matsayin mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya.
Appolonia Anaele mai muƙamin Laftanar Kanar ce za ta karɓi muƙamin daga hannun Manjo-Janar Onyema Nwachukwu.
An taƙaita zirga-zirgar babura da haramta kiwon dare a Filato Matashin da ya yi iƙirarin kashe mutane ya kai kansa ofishin ’yan sanda a KanoBayanai sun ce muƙamin nata zai fara ne a ranar Talata 22, ga watan Afrilun da muke ciki.
Shekaru sama da 50 ke nan da kafa rundunar sojin Nijeriya, kuma babu wata mace da ta taɓa riƙe wannan muƙami.
Duk da cewa kawo yanzu tana a matsayin mai riƙon muƙami ne, amma duk da haka wannan shi ne karon farko.