Bisa kididdigar da hukumar kula da harkokin fina-finai ta kasar Sin ta fitar, ya zuwa karfe 6:30 na yammacin ranar 3 ga watan Febrairun 2025, agogon Beijing, yawan kudaden da aka samu daga kallon fina-finai wato box office na sabuwar shekarar bisa kalandar gargajiyar kasar Sin ya kai yuan biliyan 8.257, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.

14, wanda ya kafa sabon tarihi. Ya zuwa yanzu dai, yawan kudaden da aka samu daga kallon fina-finan kasar Sin a 2025 yana kan gaba a kasuwar fina-finan duniya da jimillar yuan biliyan 10.121, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.4 (Mai fassara: Mohammed Yahaya)

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Hajj 2025: Hukumar Alhazai Ta Shirya Taron Bita Ga Mahajjata a Jihar Kwara

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kwara ta kammala shirye-shirye domin fara taron bita ga maniyyata aikin Hajjin bana.

Shugaban Hukumar, Alhaji Abdulsalam Abdulkadir  ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Ilori.

Ya shawarci dukkan maniyyata da su halarci wannan muhimmin shiri, yana mai  cewa za a tattauna muhimman batutuwa da suka shafi yadda ake gudanar da ibadar Hajji.

Alhaji Abdulkadir ya bayyana cewa za a fara gudanar da taron bitar ne a harabar Hukumar Jin Daɗin Alhazai  ta Jihar  daga ranar Lahadi, 20 ga watan Afirilun 2025.

Shugaban ya ƙara da cewa babban limamin masallacin Juma’a na Ilori, Sheikh Imam Mohammed Bashir, tare da wasu malaman addini daga sassa daban-daban na jihar za su jagoranci addu’a ta musamman domin samun tsaro da nasara ga maniyyatan.

 

Ali Muhammad Rabi’u 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mizanin Hada-hadar Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 5.4% A Rubu’in Farko Na Bana
  • UEFA: Mbappe Zai Jagoranci Real Madrid Yayin Da Ta Ke Fatan Kafa Sabon Tarihi A Santiago
  • Hajj 2025: Hukumar Alhazai Ta Shirya Taron Bita Ga Mahajjata a Jihar Kwara
  • Jagoran Ya Ce: Iran Ba Ta Kallon Tattaunawan Iran Da Amurka A Matsayin Kawo Karshen Takaddama A Tsakaninsu
  • Budurwar da ke rayuwa a banɗaki don gudun biyan kuɗin hayar gida
  • ’Yan Najeriya sun koka kan rashin ingancin shinkafar Gwamantin Tarayya
  • Jama’a sun koka kan rashin inganci shinkafar Gwamanti a Kogi
  • Sabon Shugaban Kasar Gabon Ya Bayyana Shiransa Na Kawo Sauyi Mai Kyau A kasar
  • Kasashen Da Mata Ba Su Taba Mulki Ba A Tarihi
  • Kamata Ya Yi Amurka Ta Kara Kokarin Gyara Kuskurenta