Bahaya A Bainar Jama’a: Za A Fara Cin Tarar N25,000 A Kano
Published: 3rd, February 2025 GMT
Majalisar dokokin jihar Kano ta zartar da wani kudirin doka da za ta ci tarar naira N25, 000 ga duk wanda aka samu ya yi fitsari, bahaya, zubar da shara ko kuma zubar da majina a kan titi ko kuma a ƙarkashin gada a jihar.
Hakan ya biyo bayan dokar da majalisar ta zartar wanda zai bai wa hukumar da ke ƙawata birane damar kula da wuraren shakatawa.
A zantawarsa da manema labarai jim kadan bayan zaman majalisar na yau Litinin, shugaban ma su rinjaye na majalisar, ɗan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Dala, Lawal Hussaini Dala, ya ce hakan ya zama dole domin bai wa gwamnati cikakken goyon bayan da take buƙata wajen tsaftace jihar Kano domin ganin ta yi kafada-da-kafada da manyan birane a duniya a fannin tsafta da ci gaba.
Lawal Hussaini ya kara da cewa, kari a kan tarar naira dubu 25, akwai hukunce-hukunce da dama a ƙarƙashin dokar ga duk wanda aka kama ya karya dokar.
এছাড়াও পড়ুন:
Dakatar da Gwamnan Ribas zubar da ƙimar Nijeriya ne a idon duniya — Jonathan
Tsohon Shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan ya ce dakatar da Gwamnan Ribas, Similanayi Fubara da aka yi kwanan nan zubar da ƙimar ƙasar ne a idon duniya.
Tsohon shugaban ya ce ba daidai ba ne dakatar da Gwamnan Ribas da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, da ’yan majalisar dokokin jihar, wanda Shugaba Bola Tinubu ya yi a makon jiya.
An ayyana zaman makoki na kwana uku bayan kashe mutum 44 a Nijar An yi wa wata karya tiyatar ceton raiChannels TV ta ruwaito Jonathan yana bayyana haka yayin da yake jawabi a matsayin shugaban taro wanda gidauniyar Haske Satumari ta shirya a ranar Asabar a Abuja.
Jonathan wanda kuma tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa ne, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan matakin na cire zaɓaɓɓun shugabanni da aka yi.
“Wannan matakin da aka ɗauka zai ɓata sunan Nijeriya ne a idon duniya,” in ji shi.
Jonathan ya ce duk da cewar akwai buƙatar ɗaukar matakan da za su magance rikicin siyasar da ya dabaibaye Jihar Ribas na tsawon lokaci, a cewarsa dakatar da waɗanda mutane suka zaɓa a matsayin shugabanninsu bai dace ba.
Ya ƙara da cewa ya san bai kamata a matsayinsa tsohon shugaban ƙasa ya cika maganganu barkatai a game da abubuwan da suke a ƙasar ba, amma “yadda ake kallon Nijeriya yana ta’allaƙa ne a kan matakan ɓangaren zartaswa da majalisa da na shari’a suka ɗauka,” in ji shi.
A farkon makon da muka yi bankwana, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa dokar ta ɓaci a Jihar Ribas, ya kuma dakatar da gwamna da mataimakiyarsa da dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.