Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-03-23@22:03:44 GMT

Muna Jaje Ga Masautar Zazzau – Manjo Janar Bello

Published: 3rd, February 2025 GMT

Kwamandan makarantar horas da sojoji dake Zaria, Manjo Janar Ahmadu Bello Mohammed ya yi alkawarin inganta dangantakar da ke tsakanin makarantar da majalisar masarautar Zazzau.

Ya bayyana haka ne lokacin da ya kai wa mai martaba Sarkin zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli ziyarar ban girma a fadar sa dake Zaria.

Manjo Janar Ahmadu Bello, wanda ya bayyana ziyarar a matsayin wani sabon babi a dangantakar daje tsakanin makarantar horas da kuratan da masarautar ta zazzau ya yi alkawarin bunkasa dangantakar dake tsakanin su,ya kuma bayyana cewa ya kai ziyarar ce domin neman albarka da hadin kan majalisar masarautar ta zazzau.

Kwamandan ya kuma mika ta’aziyar makarantar horas da kuratan sojojin ga masarautar ta zazzau bisa rasuwar daya daga cikin yan majalisar masarautar, Alhaji Rilwanu Yahaya Fate,Sarkin Yaki zazzau da ya rasu kwanan nan.

Da ya ke maida jawabi, mai martaba Sarkin zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya gode wa Kwamandan bisa ziyarar, ya kuma yi alkawarin baiwa makarantar ta Dapo duk goyon baya da hadin kai da suke bukata domin sauke nauyin dake kan su.

Mai martaban ya kara da cewa za a gudanar da tsare-tsaren da suka kamata domin daidaita batutuwan dake masarautar ta zazzau da masarautar horas da kuratan sojojin.

Haliru Hamza

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Ta aziya masarautar ta zazzau

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda ake noman gurjiya

A tattaunawarsa da Aminiya wani manomin gurjiya, Malam Muhammad Dahiru Kanda ya bayyana cewa, ya shafe sama da shekara 25 yana noman gurjiya ba tare da ya taba samun wani tasgaro ba.

Ya kara da cewa, shi noman gurjiya na da muhimminci matuka domin kuwa yana samar wa duk mai yin sa babbar riba.

Mata sun ƙwace kasuwancin kayan lambu a Gombe Mutumin da girgizar ƙasa ta razana ya shekara 2 yana zaune a cikin kogo

A cewarsa, noman gurjiya noma ne da bai sai ka tanadar masa babbar gona ba, ya danganta ne ga yadda duk ka dauke shi, amma kuma ko da rabin hekta ka dauka, ka noma, matukar ka gyara ta to kuwa ko tantama babu in Allah SWT Ya so za ka same ta a yalwace.

Haka nan in har ya kasance ka samu kasar noma mai kyau kuma mai karfi za ka samu alheri sosai wajen samun biyan bukata.

A cewarsa a duk shekara yakan samu buhunhuna biyar zuwa 7 na gurjiya a ‘yar karamar gonarsa da ba ta kai eka guda ba, wadda wannan gurjiya in ya samu yakan biya bukatunsa da na iyalansa.

Ya ci gaba da cewa, noman gurjiya na bukatar hakuri da kuma shuka ta a kan lokaci daidai da lokacin da aka fara shuka gyada domin kuwa ita gurjiya kamar gyada ce, tana bukatar shiga cikin kasa tunda ‘ya’yanta a cikin kasa take zuba su.

Haka kuma, noman gujiya in son samu ne, ka kebance mata wurinta daban komai kakantarsa, maimakon ka shuka ta cikin gero ko dawa ko kuma hada ta cikin gyada domin in ka kebance wajen shuka ta daban, takan fi haihuwa da yawa sabanin shuka ta hade da wasu amfanin gona, kana tana bukatar a dan sa takin gida ko na zamani.

Don haka a gaskiya noman gujiya na da matukar muhimmanci domin kuwa yakan samar wa manoma alherin da ba ya misaltuwa, musamman ganin cewar gurjiya na da matukar daraja a kasuwa.

A yanzu haka buhun gurjiya mai nauyin kilo 50 kudinsa ya kai kimanin Naira dubu 55 zuwa dubu 60.

Baya ga haka kuma akwai bukatar manomi in ya zo shuka gurjiya, ya zabo iri mai kyau ba irin da zai tsumbure ba domin samun yalwarta.

“Yin hakan na daga cikin abin da ke taimaka min da ma sauran manoma wajen samun gurjiya mai yawa in lokacin cire ta ya yi, kuma matukar manomi na son amfana da ita a kaka, to kuwa ya guji yawan cire ta da danyentakarta tun ba ta kai ga kosawa ba, don sayarwa.

Sai dai in ba bukatar hakan ne ta taso ba, domin ni sau tari nakan hakura ne da cirar ta in tana danya illa daga lokaci zuwa lokaci nakan cira don kai wa iyali su dafa, su ci.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda ake noman gurjiya
  • Sudan: Sojoji na ci gaba karbe mahimman gine-gine a birnin Khartoum
  • Gwamnatin Jigawa Ta Nanata Dokar Haramta Kiwon Dare
  • Masarautar Bauchi Ta Sauya Shawara: Za A Yi Hawan Daushe
  • Ba Gwamna Bala Ne Ya Soke Hawan Daushe Ba – Masarautar Bauchi Ta Bayyana Gaskiya
  • Kasar Sin Ta Bayar Da Rijiyoyin Burtsasai 66 Ga Al’ummomin Zimbabwe Dake Fama Da Karancin Ruwa
  • El-Rufa’i Ya Yi Kadan Ya Sa Mu Bar Jam’iyyar PDP – Sule Lamido
  • An Yi Tarukan Tattaunawar Kasa Da Kasa Kan More Damammakin Sin A Havana Da Doha
  • Jiragen Yakin HKI Sun Kai Hare-Haren Kan Wasu Wurare A Gabaci Da Kuma Kudancin Kasar Lebanon
  • Hajjin Bana: Maniyata 3, 155 Suka Yi Rijista a Kano