Zargin Almundahanar Miliyan 90.4: EFCC Ta Gurfanar Da Tsohon Shugaban Hukumar NHIS
Published: 4th, February 2025 GMT
Zargin Almundahanar Miliyan 90.4: EFCC Ta Gurfanar Da Tsohon Shugaban Hukumar NHIS.
এছাড়াও পড়ুন:
Hajjin 2025: Shirye-shirye Sun Yi Nisa A Jihar Jigawa
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce shirye-shirye sun yi nisa game da aikin Hajjin shekarar 2025 a jihar.
Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ne ya bayyana hakan ga Radio Nigeria a hedikwatar hukumar da ke Dutse.
A cewarsa, zuwa yanzu hukumar ta mika sunayen maniyyata fiye da dubu ɗaya da suka kammala biyan kuɗin aikin Hajji daga jihar zuwa ga Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON).
Ya ce tuni aka fara shigar da waɗanda suka kammala biyan kuɗin cikin tsarin neman biza.
Labbo ya bayyana cewa hukumar ta biya Hukumar Hajji ta Ƙasa kuɗi naira biliyan takwas a madadin alhazan jihar na shekarar 2025.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce ana gudanar da tarukan bita ga maniyyata a kullum, a kananan hukumomi 27 na jihar, ta hannun wasu malamai don ilmantar da su game da aikin hajjin.
Ya ƙara da cewa hukumar za ta raba jakunkuna da za su daukin nauyin kilo 8 da unifom ga jami’an yankuna da cibiyoyi domin rabawa mahajjatan.
Shugaban hukumar ya ja hankalin maniyyatan da su riƙa halartar traon bita saboda muhimmancinsa.
Ya yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa goyon baya da haɗin kai da yake ba hukumar domin samun nasarar gudanar da aikin hajji ba tare da wata tangarda ba.
Radio Nigeria ta ruwaito cewa Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta ware kujeru sama da 1,800 ga jihar domin aikin hajjin bana.
Usman Muhammad Zaria