An yi kiyasin adadin tafiye-tafiyen fasinjoji tsakanin yankuna zai kai biliyan 4.8 a duk fadin kasar Sin daga ranar 14 ga watan Janairu zuwa ta 2 ga watan Febrairu, wato rabin farko na kwanaki 40 na zirga-zirgar bikin bazara. 

Adadin ya nuna karuwar kashi 7.2 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara, a cewar tawagar aiki ta musamman da aka kafa don saukake ayyukan da suka shafi zirga-zirgar bikin bazara, wanda aka fi sani da chunyun.

Hukumar FCTA Ta Rufe Asibitin Da Ke Aiki Ba Bisa Ka’ida Ba A Kuje Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Athletico Madrid Da Getafe

Zirga-zirgar fasinjoji ya karu tun daga ranar 30 ga watan Janairu, inda adadin tafiye-tafiyen ya zarce miliyan 300 a ranakun 31 ga watan Janairu da ta 1 ga watan Fabrairu, duk sun zarce na bara, a cewar wata cibiyar bincike da ci gaba karkashin ma’aikatar sufuri, tana mai cewa ana sa ran hakan na iya ci gaba da faruwa a lokacin hutun.

Har ila yau, a ranar 2 ga Fabrairu kadai, an yi kiyasin adadin tafiye-tafiye zai kai miliyan 319.32, tare da manyan tituna da ke da kaso mafi girma na tafiye-tafiye miliyan 301.02, a cewar tawagar aiki ta musamman. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Ƴansandan Sun Gayyaci Sanata Karimi Kan Zargin Shigar Kungiyar Leƙen Asirin Rasha Majalisa’

Ƴansandan sun gayyaci Sanata Sunday Karimi domin bayani kan zarginsa na cewa ƙungiyar leƙen asirin ƙasar Rasha ta KGB ta samu shiga cikin Majalisar Dokoki, wanda ke barazana ga tsarin dimokuraɗiyya a Nijeriya.

Zargin ya samo asali ne daga rahoton da Sanata Karimi ya raba akan ƙungiyar ta WhatsApp a Majalisar Dattijai a ranar 23 ga Fabrairu, 2025. Rahoton, wanda aka wallafa ta gidan jaridar The Reporters, ya jawo ce-ce-ku-ce a cikin Majalisar, inda Sanata Natasha H. Akpoti-Uduaghan, wacce aka dakatar, ta shigar da buƙatar yin bincike ga Shugaban ‘Yansanda.

Fiye Da Dalibai 4,200 Suka Amfana Da Tallafin Ilimi Na Sanata Solomon Adeola Kotu Ta Dakatar Da INEC Karɓar Buƙatar Yin Kiranye Ga Senata Natasha

A cikin ƙarar da ta fitar a ranar 5 ga Maris, 2025, Sanata Akpoti-Uduaghan ta nuna damuwa kan wannan batu, tana bayyana cewa irin wannan zargi yana ɗauke da barazana mai girma ga tsaron ƙasa da kuma buƙatar gaggawar yin bincike. Ta yi kira da cewa wannan batu ba za a iya watsar da shi ba, domin ya shafi dimokuraɗiyya da tsaron ƙasa.

Sanata Karimi, wanda aka gayyace shi don yin ƙarin bayani kan rahoton da ya yaɗa, zai yi amsa tambayoyi a shalƙwatar ‘Yansanda a Abuja a ranar 24 ga Maris, 2025.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ƴansandan Sun Gayyaci Sanata Karimi Kan Zargin Shigar Kungiyar Leƙen Asirin Rasha Majalisa’
  • Iran da Masar sun tattauna kan rikicin da Isra’ila ta jefa yankin gabas ta tsakiya
  • NAJERIYA A YAU: Yadda watan Ramadana ke tasiri a harkokin kasuwanci
  • Gombe Za Ta Kashe Naira Biliyan 1.1 Don Samar Da Fitilun Hanya Masu Aiki Da Hasken Rana
  • Masarautar Bauchi Ta Sauya Shawara: Za A Yi Hawan Daushe
  • Fashin Baki Kan Kasafin Kudin 2025 Na Naira Tiriliyan 54.99
  • Putin Ya Aike Wa Ayatullah Khamenei Da Murnar Idin Nowruz
  • Dangote Zai Gina Sabuwar Masana’antar Siminti A Jihar Ogun
  • Mace ta farko ta zama shugabar ƙasar Namibia
  • An Zabi ‘Yan Kasar Zimbabwe  Kuma Mace Ta Farko A Matsayin Shugabar Shugabar Kwamitin  Wasannin Olympic