Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Kano
Published: 4th, February 2025 GMT
Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wasu mutum biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda laifin lashe wata dattijuwa mai shekara 67, kan zargin ta da maita.
Kotun ya yanke musu hukuncin kisa ne a ranar Litinin bayan samun su da laifin kiran dattijuwar mai suna Ɗahare Abubakar, mayya sannan suka daɓa mata wuka har lahira.
Mai Shari’a Usman Maido, ya bayyana cewa masu gabatar da ka to sun gabatar da gamsassun hujjoji da suka tabbatar da laifin wadanda aka gurfanar.
Waɗanda kana yanke wa hukuncin kisan su ne Da’luta Ibrahim, Abdulaziz Yahaya, Faisal Yahaya, Ibrahim Abdu da Ayuba Abdulrahman.
Mai gari ya tsere bayan mazauna sun cinna wa gidansa wuta a Kano Rikicin rusau ya yi ajalin mutum 4 a Kano NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Za Mu Kashe Biliyan N2.5 Kan Auren Zawarawa —Gwamnatin KanoTun da farko, mai gabatar da kara, Lamiɗo Abba-Soronɗinki, ya shaida wa koyon cewa da misalin karfe 8.30 na safiyar ranar 23 ga watan Nuwambar shekarar 2023 ne waɗanda ake tuhumar suka hada baki wajen yin aika-aikan.
Ya ce bayan waɗanda ake tuhumar sun zargi Marigayiya Ɗahare da maita ne suka bi ta gona ɗauke da makamai, suka yi mata kisan gilla,
Ya ce an garzaya da ita zuwa Babban Asibitin Wudil inda likitoci suka tabbatar cewa ran dattijuwar ya yi halinsa.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Daɗin Kowa da ke Ƙaramar Hukumar Wudil.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: dattijuwa
এছাড়াও পড়ুন:
Faransa ta jaddada aniyarta na ci gaba da tattaunawar nukiliyar iran
Kasar faransa ta jaddada anniyar na ci gaba da tattaunawa kan shirin nukiliyar iran.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Faransa ya bayyana a ranar Alhamis cewa, Faransa na ci gaba da jajircewa wajen ganin an warware matsalar nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya, kuma a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da Tehran.
A yayin taron manema labarai na mako-mako a birnin Paris, Christophe Lemoine ya jaddada cewa: “Muna ci gaba da jajircewa wajen warware matsalar nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya, kuma a shirye muke mu ci gaba da tattaunawa da Tehran.”
Wannan bayanin na zuwa ne bayan da ministan harkokin wajen Iran Seyyed Abbas Araghchi ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na X cewa, Tehran a shirye ta ke ta ci gaba da tattaunawa da kasashen Turai, inda ya bayyana cewa tattaunawar za ta iya bude wata sabuwar hanya.
Araghchi ya bayyana cewa, bayan shawarwarin baya-bayan nan da aka yi a Moscow da Beijing, a shirye yake ya ziyarci Paris, Berlin da London.
Ya kuma ce tun kafin fara tattaunawar da Amurka, Iran na shirye, amma kasashen Turan uku da batun ya shafa ba su nuna sha’awarsu ba.