Asensio Ya Kammala Komawa Aston Villa Daga PSG
Published: 4th, February 2025 GMT
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Aston Villa ta kammala ɗaukar tsohon ɗan wasan Real Madrid Marco Asensio daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta PSG a matsayin aro zuwa ƙarshen kakar wasa ta bana.
Asensio wanda ya bar Real Madrid a shekarar 2023 ya na ɗaya daga matasan ƴan wasa da tauraruwarsu ke haskawa a harkar ƙwallon ƙafa a yanzu.
Aston Villa ta wallafa a shafinta na kafar sadarwa cewa Asensio ya rattaɓa hannun komawa ƙungiyar a matsayin aro daga PSG har zuwa ƙarshen kakar wasa ta bana.
Asensio ne ɗan wasa na biyu da Villa ta ɗauka aro bayan Marcus Rashford wanda ta aro daga Manchester United yayin da ake gab da rufe kasuwar saye da sayarwar ƴan ƙwallo a nahiyar Turai.
এছাড়াও পড়ুন:
Hajj 2025: Hukumar Alhazai Ta Shirya Taron Bita Ga Mahajjata a Jihar Kwara
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kwara ta kammala shirye-shirye domin fara taron bita ga maniyyata aikin Hajjin bana.
Shugaban Hukumar, Alhaji Abdulsalam Abdulkadir ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Ilori.
Ya shawarci dukkan maniyyata da su halarci wannan muhimmin shiri, yana mai cewa za a tattauna muhimman batutuwa da suka shafi yadda ake gudanar da ibadar Hajji.
Alhaji Abdulkadir ya bayyana cewa za a fara gudanar da taron bitar ne a harabar Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar daga ranar Lahadi, 20 ga watan Afirilun 2025.
Shugaban ya ƙara da cewa babban limamin masallacin Juma’a na Ilori, Sheikh Imam Mohammed Bashir, tare da wasu malaman addini daga sassa daban-daban na jihar za su jagoranci addu’a ta musamman domin samun tsaro da nasara ga maniyyatan.
Ali Muhammad Rabi’u