Kungiyar Hamas wacce take iko da yanin zirin gaza ta bada sanarwan cewa a shirye take, masu shiga tsakanin, wato kasar Masar ta fara tattaunawa marhala ta biyu na tattaunawar tsagaita wuta a Gaza. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto kamfanin dillancin laran AFP na kasar Faransa yana fadar haka.

Ya kuma kara da cewa, wani jami’in kungiyar wanda baya son a bayyana sunansa ya ce kungiyar a shirye take a fara tattaunawar.. A wannan tattaunawa dai ana saran za’a fayyace filla-filla kan yadda al-amura zasu kasance a nan gaba a zirin gaza. Labarin ya kara da cewa jami’an Hamas sun bayyana haka ne a ranar da aka yi musayar fursinoni da HKI a garin Khan Yunus. A ranar 1 ga watan Fabrairun shekara ta 2025.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Sojojin Yemen Sun Kakkabo Jirgin Yakin Amurka Wanda Ake Sarrafa Shi Daga Nesa Na 19

Sojojin kasar Yemen sun kakkabo jirgin yakin Amurka wanda ake sarrafashi daga nesa samfurin MQ-9 na 19 a jiya Lahadi da yamma a sararin samaniyar kasar.

Tashar talabijan ta Presstv daga nan Tehran ya bayyana cewa sojojin kasar ta Yemen sashen UAV wato masu kula da abinda ake kira ‘Drones’ sun bada sanarwan kakkabo jirgin yaki na Amurka ne a lokacinda yake tattara bayanai a wasu yankuna a sararin samaniyar kasar.

Masana sun bayyana cewa farashin ko wane jirgi yakin samfurin MQ-9 ya kai dalar Amurka miliyon $33, don haka ya zuwa yanzu kasar Amurka ta yi asarar dalar Amurka miliyon $600.  Kafin haka dai sojojin Yemen bangaren makamai masu linzami sun bada sanarwan cilla makamai masu linzami samfurin Balistic  guda biyu kan HKI, wanda ya kai ga rufe tashar jiragen sama na Bengerion a birnin Yafa (telaviv.) . Bugediya Yahyah Saree kakakin sojojin kasar ta Yemen ya bayyana cewa godiya ta tabbata ga All..saboda dukkan makaman sun cimma manufofin cillasu, wadanda suka hada da rufe tashar jiragen sama na Bengrion da tilastawa miliyoyin yahudawan sahyoniyya gudu zuwa wuraren buya.

Saree ya kammala da cewa, ayyukan soje a kan HKI da kuma Amurka zasu ci gaba har zuwa dakatar da yaki a Gaza.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojojin Yemen Sun Kakkabo Jirgin Yakin Amurka Wanda Ake Sarrafa Shi Daga Nesa Na 19
  • Kasashen Larabawa Na Yankin Tekun Farisa Sun Yi Fatan Al-Khairi Ga Iran Da Amurka A Tattaunawar Shirin Nukliyar Kasar
  • Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci: Makiya Suna Hasadan Ci Gaban Kasar Iran
  • Gwamnatin Amurka Ta Yi Da’war Cewa; Ba Ta Neman Tashin Hankali Tsakaninta Da Iran
  • Dagewa Iran Takunkuman Zalunci Na Daga Cikin Manufofin Tattaunawa Da Amurka: Aref
  • Sharhi: Tattaunawa Zagaye Na Farko Tsakanin Iran Da Amurka A Oman
  • Iran da Amurka zasu ci gaba da tattaunawa a mako mai zuwa
  •  Limamin Tehran: Iran Ba Ta Tsoron Tattaunawa
  • MDD: Mafi Yawancin Wadanda Yaki Ya Ci A Gaza Mata Ne Da Kananan Yara
  • Saudiya Tace Shigo Da Agaji Cikin Gaza Bai Da Dangantaka Da Tsagaita Wuta