HausaTv:
2025-03-23@22:11:29 GMT

Trump Yace Saukar Farashin Man Fetur Zai Iya Kawo Karshen Yakin Ukraine

Published: 4th, February 2025 GMT

Shugaban kasar Amurka donal Trum ya bayyana anniyarsa na aiki tare da kungiyar kasashen masu arzikin man fetur don rage farashin man fetur a duniya. Shugaban ya bayyana cewa zai yi aiki da kasar Saudiya UAE da sauransu don rage farashin man man fetur a duniya. Kuma daga nan yana ganin aka iya kawo karshen yakin da ke faruwa a kasar  Ukrain.

Shugaban ya fadi haka ne a jawabinda da ya gabatar a taron tattalin arzikin da aka gudanar a Davos na kasar Swizziland. Duk tare da tattaunawa ta abokantaka da kuma bukatar a a kara yawan man fetur a kasuwannin duniya, zuwa dalar Amurka triliyon guda.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Moscow : Dole ne Rasha da China su shiga tattaunawar nukiliya da Iran

Kasar Rasha ta bayyana cewa dole Moscow da Beijing su shiga shawarwarin tattaunawar nukiliya da Iran.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta bayyana cewa, Moscow a shirye take ta samar da ingantacciyar hadin gwiwa da dukkan bangarorin kan batun yarjejeniyar nukiliyar Iran. “

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa ya aike da wasika zuwa Tehran domin fara tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran; yayin da shi da kansa ya fice daga yarjejeniyar nukiliyar Iran a wa’adinsa na farko.

A halin da ake ciki dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta mayar da martani ga wasikar shugaban Amurka Donald Trump a cikin kwanaki masu zuwa ta hanyoyin da suka dace.

Araghchi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi kai tsaye a gidan talabijin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRIB) ranar Alhamis.

Araghchi ya kuma lura cewa a wannan karon, ci gaban ya zo tare da wani yunkuri na diflomasiyya daga Amurkawa, ciki har da wasika da bukatar yin shawarwari.

Ya kuma bayyana cewa manufar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a bayyane take. “Ba za mu shiga tattaunawa kai tsaye karkashin matsin lamba, barazana, ko karin takunkumi.”

Ministan harkokin wajen kasar ya kuma bayyana cewa wasikar “mafi yawan barazana ce,” amma kuma akwai damamaki a ciki.

A farkon watan Maris ne Trump ya bayyana cewa ya rubuta wasika zuwa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gobara ta tashi a gidan mai sakamakon fashewar tanka a Neja
  • Al-Huthi Ya Ce Kawo Wani Jirgin Ruwa Mai Daukar Jiragen Saman Yaki Gazawa Ce Ga Amurka
  • Moscow : Dole ne Rasha da China su shiga tattaunawar nukiliya da Iran
  • Ranar Mata Ta Duniya: NPA Ta Mayar Da Hankali Wajen Kare ‘Yancin Mata –Dantsoho
  • Trump Ya Bayyana Dalilin Rufe Gidan Rediyon Muryar Amurka
  • Iran da UAE sun kirayi Isra’ila da Amurka da su kawo karshen hare-harensu a Gaza da Yemen
  • Saree: Filin jirgin saman Ben Gurion ba shi da aminci har sai an kawo karshen yakin Isra’ila a Gaza
  • Jiragen Yakin HKI Sun Kai Hare-Haren Kan Wasu Wurare A Gabaci Da Kuma Kudancin Kasar Lebanon
  • Araghchi : Iran za ta mayar da amsa ga wasikar Trump cikin kwanaki masu zuwa
  • Zargin Kisan Kiristoci A Nijeriya: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Watsi Da Rahoton Amurka