Jeremy Corbyn Ya Bukaci Ganin An Hukunta Isra’ila Da Masu Ba Ta Makamai Akan Kisan Kiyashin Falasdinawa
Published: 4th, February 2025 GMT
Tsohon shugaban jam’iyyar “ Labour” ta Birtaniya Jeremy Corbyn ya yi kira da a hukunta Isra’ila, da masu daukar nauyinta akan kisan kiyashin da ta yi tun bayan ranar 7 ga watan Okotoba 2023.
Cobyn ya rubuta a shafinsa na X cewa; A cikin bayan nan ne zurfin barnar da Isra’ila ta yi, yake kara bayyana, don haka wajibi ne jami’anta su fuskanci shari’a akan kowane rai daya da aka yi asararsa.
Cobyn ya ci gaba da cewa; Duk wanda ma ya rika aikewa da makamai yana sane da cewa za a yi amfani da su a yi kisan kiyashi, shi ma a hukunta shi.”
A cikin watanni shida da su ka gabata Birtaniya ta sayar wa da HKI makamai na biliyoyin Fam, kuma da akwai rahotanni da suke nuni da cewa an yi amfani da su a kisan kiyashin da aka yi wa al’ummar Falasdinawa.
Tun farkon yakin Gaza a watan Oktoba 2023, al’ummar kasar Birtaniya ta kasance a gaba-gaba wajen gudanar da Zanga-zangar yin tir da HKI da kisan kiyashin da take yi wa al’ummar Falasdinu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Da Sifaniya Sun Daga Matsayin Hadin Gwiwa A Fannin Shirya Fina-finai
Wannan gargadi da Sin da EU suka gabatar ga manyan kamfanonin shirya fina-finai da na fasaha na Amurka, na nuna cewa, gangancin da gwamnatin Amurka ke yi na kakaba haraji barkatai, zai ci gaba da illata kashin bayan fannoninta na cinikayya.
Hadin gwiwa tsakanin Sin da Sifaniya, ya kara bayyana yadda Sin ke fatan ci gaba da bude kofarta, da aiki tare da abokan hulda irinsu Sifaniya wajen goyon bayan tsarin cudanyar sassa daban daban, da goyon bayan dunkulewar salon raya tattalin arziki da cinikayya marar shinge, da samar da karin hidimomi, da kayayyaki masu inganci ga kasashen biyu ta hanyar hadin gwiwa da juna, da mutunta juna, da amfanar da al’ummunsu. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp