Aminiya:
2025-02-22@06:19:01 GMT

Dalilin da Tinubu ya ƙi amincewa da ƙudirin kafa Jami’ar Ilimi a Adamawa

Published: 4th, February 2025 GMT

Shugaba Bola Tinubu ya ƙi rattaba hannu kan ƙudirin kafa Jami’ar Ilimi ta Tarayya a Numan da ke Jihar Adamawa.

Hakan na ƙunshe cikin wata wasiƙa da ya aike wa Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas wadda mataimakinsa, Benjamin Kalu ya karanta a yayin zaman majalisar na yau Talata.

Alakarmu da El-Rufai na nan babu matsala —Uba Sani HOTUNA: Hatsarin tirela ya yi ajalin mutum 4, shanu 15 da awaki 20 a Neja

Wasiƙar shugaban ta kare matakin da ya ɗauka na ƙin amincewa bisa la’akari da tanadin da sashe na 22 da ke cikin ƙudirin kafa jami’ar ya yi.

Ya yi bayanin cewa sashen ya yi tanadin cewa filin da za a gina jami’ar zai kasance a ƙarƙashin ikon Gwamnatin Jihar Adamawa wanda ya saɓa wa ƙa’idar kasancewa a ƙarƙashin ikon Gwamnatin Tarayya.

Kazalika, wasiƙar ta Shugaba Tinubu ta kafa hujjar cewa sashe na 25 (b) da ke ƙunshe a cikin ƙudirin bai bayyana cewa jami’ar tana da hurumin da za ta riƙa bayar da shaidar karatun digiri ba.

Idan ba a manta ba, a shekarar da gabata ce Majalisar Wakilan ta amince da ƙudirin kafa Jami’ar Ilimi a Numan da ke Jihar Adamawa kuma ta miƙa wa shugaban ƙasar domin neman sahalewarsa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jami ar Ilimi ta Tarayya Jihar Adamawa

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan sanda sun daƙile satar mutane, sun kama wasu 3 a Borno

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta daƙile wani yunƙuri da ’yan bindiga suka yi na sace wani mutum a Sabon Garin Lassa da ke Ƙaramar Hukumar Askira Uba.

Rundunar ta kuma cafke wasu mutum uku tare da ƙwato wata bindiga ƙirar gida a hannunsu.

Babban mai kai wa Bello Turji makamai ya shiga hannu NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ba Za Mu Sauke Farashin Burodi Ba —’Yan kasuwa

Majiyoyin tsaro sun shaida wa Zagazola Makama cewa, lamarin ya faru ne a ranar 20 ga watan Fabrairu da misalin karfe 1 na dare.

Wasu ’yan bindiga huɗu suka kai hari gidan Mohammed Abubakar, mazaunin Sabon Gari Lassa, da nufin sace shi.

“Wanda suka yi niyyar sacewa ya yi ƙoƙarin kare kansa da adda, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa ba tare da sun cimma burinsu ba”, in ji majiyar.

Bayan haka, Abubakar, ya gaggauta kiran ’yan sanda, inda tare da haɗin gwiwar ’yan banga, jami’an tsaro suka bi sahun ’yan bindigar zuwa maɓoyarsu.

A sakamakon haka, rundunar ‘yan sanda ta cafke mutum uku da ake zargi, dukkaninsu mazauna ƙauyen Gajali da ke Ƙaramar Hukumar Askira Uba.

“Haka kuma an ƙwato wata bindiga da aka ƙera a gida daga hannun waɗanda ake zargin,” in ji majiyar.

Rundunar ’yan sandan jihar, ta yaba da yadda jami’an tsaro suka mayar da martani cikin gaggawa, tare da yin kira ga al’umma da su kasance masu lura da duk wani abu da ba su saba gani ba.

Ta kuma buƙaci su gaggauta kai rahoto ga jami’an tsaro domin ɗaukar mataki a kan lokaci.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan sanda sun daƙile satar mutane, sun kama wasu 3 a Borno
  • Babban Jami’i A Kungiyar JIhadul-Islami Ya Ce: Gudumawar Marigayi Sayyid Hasan Nasrullahi Ba Zai Fadu Ba
  • Jihar Kano Ta Samar Da Wani Salo Na Bunkasa Ilmin Addinin Musulunci A Jihar
  • Shugaba Tinubu Ya Yaba Da Gudunmawar Da IBB Ya Bayar Yayin Mulkinsa
  • An rufe Jami’ar Kogi saboda zanga-zangar ɗalibai
  • Jami’an tsaron al’umma 6 sun mutu a artabu da ’yan bindiga a Sakkwato
  • Jami’in tsaron al’umma 6 sun mutu a artabu da ’yan bindiga a Sakkwato
  • NAJERIYA A YAU: Tanadin Dokar Kasa Kan Kirkirar Gwamnatin Bibiya A Kano
  • Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Kwalejin Koyon Tukin Jiragen Sama
  • Ma’aikatar sharia ta kasar Iran Ta bada sanarwan Kama Yan Kasar Burtaniya 2 Tare Da Tuhumar Leken Asiri