Hamas Ta Ce An Fara Shawarwarin Tsagaita Wuta A Mataki Na Biyu
Published: 4th, February 2025 GMT
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta sanar da fara shawarwarin tsagaita wuta a mataki na biyu tsakaninta da Isra’ila.
Kakakin Abdul Latif al-Qanou ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a kafar sadarwar zamani.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a tashar ta Telegram mai magana da yawun kungiyar Abdel Latif al-Qanoua ya zargi Isra’ila da “jinkirta aiwatar da ka’idojin jinƙai a yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma dakatar da aiwatar da hukuncin kisa.
Ya ce har yanzu kungiyar Falasdinu ta damu da batutuwa da dama da suka hada da matsuguni ga mutanen Gaza, da kuma kayan agaji da kuma kokarin sake gina yankin.
Al-Qanou ya kuma zargi Isra’ila da “katse” ka’idojin jin kai da ke kunshe cikin yarjejeniyar tsagaita bude wuta da jinkirta” aiwatar da su.
Isra’ila ta ce ta aike da wata tawaga domin tattaunawa a mataki na gaba a tsagaita wuta mai rauni da kungiyar Hamas, wanda ke nuni da yiwuwar samun ci gaba gabanin ganawar firaminista Benjamin Netanyahu da shugaban Amurka Donald Trump a ranar Talata.
Bayanai sun ce Isra’ila ta ci gaba da keta yarjejeniyar ta hanyar kai hare-hare Gaza.
Isra’ila ta kama Falasdinawa akalla 380 tun bayan tsagaita bude wuta a Gaza inji kungiyoyi masu zaman kansu akasarinsu matasa a yankin Yammacin Gabar Kogin Jordan da aka mamaye tun bayan da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza ta fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasashen Larabawa Na Yankin Tekun Farisa Sun Yi Fatan Al-Khairi Ga Iran Da Amurka A Tattaunawar Shirin Nukliyar Kasar
Babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa na yankin tekun Farisa (PGCC) ya yi fatan alkhairi ga kasashen Iran da Amurka a tattaunawa ba kai tsaye ba a tsakaninsu dangane da shirin Nukliya ta kasar Iran na zaman lafiya wanda suka fara, a birnin Mascat na kasar Omman a ranar Asabar da ta gabata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jasem Mohamed AlBudaiw yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa, kungiyar tana bukatar gidan an warware matsaloli tsakanin kasashen duniya ta hanyar tattanawa. Haka ma tsakanin kasashen yankin.
AlBudaiw ya yabawa kasar Omman da shirya wannan tattaunawar, sannan ya yi fatan tattaunawan da aka fara zai kai ga rage tada jijiyoyin wuya a yankin da kuma kasashen duniya, ya kuma ce kasashen yankin suna fatan zasu kai ga sakamako mai kyau tsakanin kasashen biyu.
Gwamnatin kasar Iran dai tana har yanzun suna shakkar kasar Amurka saboda yawan yaudarar da tayiwa kasar a baya. Musamman fitar kasar daga yarjeniyar JCPOA a shekara ta 2018. Da kuma yawan takunkuman da ta dorawa a kasar tun lokacin.
Daga karshe babban sakataren kungiyar ta PGCC ya ce tana fatan za’a kawo karshen duk wani rikici a gabas ta tsakiya daga ciki har da na HKI a falasdinawa a Gaza ta hanyar tattaunawa da fahintar Juna.