Shamkhani : Iran Za Ta Kare Shirinta Na Nukiliya Na Zaman lafiya Da Dukkan Karfinta
Published: 4th, February 2025 GMT
Babban mai ba da shawara kan harkokin siyasa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa Iran za ta yi amfani da dukkan karfinta wajen kare shirinta na nukiliya cikin lumana.
A yayin wata ziyara da ya kai wani baje kolin da ke nuna sabbin nasarorin da aka samu a masana’antar nukiliya a hukumar makamashin nukiliya ta Iran (AEOI) a ranar Litinin din nan, Ali Shamkhani ya sake nanata gaskiyar shirin nukiliyar Iran da kuma yadda kasar ke bin ka’idojin kasa da kasa.
“Iran ba ta taba neman makaman nukiliya ba kuma ba za ta taba yin hakan ba,” in ji shi. “Duk da haka, tana kare hakkinta da dukkan karfinta.”
Shamkhani ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kuduri aniyar kare muradun al’ummar Iran daga wuce gona da iri na manyan kasashen duniya, wadanda suka yi watsi da alkawuran da suka dauka.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Trump Ya Danganta Zelensky Da Dan Mulkin Kama Karya
Shugaban Amurka Donald Trump ya danganta takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky da “mai mulkin kama karya,” yana mai bukatarsa da ya gaggauta daukar matakin tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya da Rasha ko kuma ya yi kasadar rasa kasarsa.
Trump ya yi wadannan kalamai ne, kwana guda bayan da ya zargi Ukraine da haddasa yakin Rasha, yana mai cewa hakan ya janyo Washington cikin rikicin na shekaru uku.
An shirya wa’adin shekaru biyar na Zelensky zai kare a watan Mayun 2024, amma saboda dokar soja da aka kafa a watan Fabrairun 2022, ba za a iya gudanar da zabe ba.
Kalaman na Trump sun jawo martani cikin gaggawa daga jami’an Ukraine, inda ministan harkokin wajen kasar Andrii Sybiha ya jaddada cewa babu wanda zai tilasta wa kasarsa mika wuya. “Za mu kare hakkinmu na wanzuwa,” in ji shi a X.
A martanin da Zelensky ya mayar, ya zargi takwaransa na Amurka da rashin fahimtar Kremlin game da rikicin.
Bayan Kama mulki Trump, ya sauya manufofin Amurka kan Ukraine, inda ya kawo karshen yunkurin mayar da Rasha saniyar ware tare da yin shawarwari kai tsaye da shugaban Rasha Vladimir Putin.