Daminar Bana: NiMet Ta Yi Hasashen Jinkirin Saukar Ruwan Sama A Jihohin Arewa.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Tarayya Ta Bai Wa Jihar Jigawa Kayayyakin Noma Na Sama Da Naira Biliyan 5

Gwamnatin tarayya ta ce ta bai wa gwamnatin jihar Jigawa tallafin kayayyakin noma na sama da naira biliyan 5 domin bunkasa noman abinci a fadin jihar.

 

 

Ministan noma da samar da abinci Sanata Abubakar Kyari ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a garin Dabi da ke karamar hukumar Ringim a bikin ranar manoman alkama ta bana.

 

Ya bayyana cewa, matakin na daga cikin kudirin gwamnatin tarayya na tallafawa jihar wajen bunkasa noma domin kasuwanci.

 

Sanata Kyari ya yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya ta gamsu sosai da yadda gwamnatin jihar Jigawa da manoma suka yi, na rungumar ayyukan noman rani.

Ministan ya yaba da kokarin gwamnatin jihar Jigawa da manoma, bisa goyon bayan shirin gwamnatin tarayya na bunkasa noman alkama,  ta hanyar samar da kayan amfanin gona da dabarun zamani.

A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na bullo da wasu tsare-tsare da za su samar da guraben ayyukan yi da wadata kasa da abinci.

A cewarsa, tuni ya sayo taraktoci 300, ingantattun irin shuka, da sauran kayayyakin aikin gona domin noman amfanin gona daban-daban a fadin kananan hukumomin jihar 27.

Tun da farko a jawabinsa na maraba kwamishinan noma da albarkatun kasa na jihar Alhaji Muttaqa Namadi ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta bayar da tan 3,500 na ingantaccen irin alkama, da injinan ban ruwa 10,000 domin tallafawa noman alkama a jihar.

Ministan da mukarrabansa da Gwamna Umar Namadi sun ziyarci gonakin alkama da dama a Yakasawa da Dabi a karamar hukumar Ringim.

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, kayayyakin da gwamnatin tarayya ta bayar sun hada da injinan ban ruwa 10,000, da lita 10,000 ta maganin kwari, taki na ruwa da injinan feshi.

Wasu daga cikin manyan baki da suka halarci bikin sun hada da, Darakta Janar na Gidan Rediyon Tarayya FRCN, Dr Mohammed Bulama,  da sarakuna da malaman addini, da wakilan kungiyar sarrafa fulawa ta kasa, da manoman alkama da wasu manyan jami’an gwamnati.

Usman Muhammad Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tashar Jiragen Sama Ta Rafikul Hariri Int. Na Birnin Beirut Yana Ciki Da Masu Shiga Kasar Saboda Jana’izar Shaheed Nasarallah
  • NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ba Za Mu Sauke Farashin Burodi Ba —’Yan kasuwa
  • Harin ’Yan bindiga: Mun yi asarar shanu sama da miliyan 4 – Miyetti Allah
  • Gidauniyar Tunawa Da Sir Ahmadu Bello Za Ta Gudanar Da Taronta Karo Na 11 A Bauchi.
  • Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Kwalejin Koyon Tukin Jiragen Sama
  • ’Yan bindiga sun Kashe mutum 2 kan jinkirin biyan kuɗin fansa
  •  Rasha Ta Kakkabo Jiragen  Sama Marasa Matuki 9 Na Kasar Ukiraniya
  • Gwamnatin Tarayya Ta Bai Wa Jihar Jigawa Kayayyakin Noma Na Sama Da Naira Biliyan 5
  • Za a binciki INEC kan jinkirin gudanar da zaɓen cike giɓi