Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za ta karfafa kyakkyawar alakar da ke tsakaninta da asusun horar da ma’aikata ITF.

Shugaban ma’aikata na jihar Alhaji Muhammad K Dagaceri ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban asusun horas da ma’aikata na yankin arewa maso yamma, Malam Aminu Abdu a ofishinsa.

A cewarsa, gwamnatin jihar tana sane da muhimmancin da asusun ke da shi,  musamman ga ma’aikatan da aka horas da su domin samun kwarewa a fanninsu.

Dagaceri, ya tabbatar wa shugaban asusun cewa, gwamnatin jihar za ta ci gaba da bayar da dukkan goyon baya da hadin kai ga sabon ofishin na ITF da aka kafa a yankin Jigawa.

Tun da farko, Shugaban Asusun na Arewa maso Yamma, Malam Aminu Abdu ya ce sun kawo ziyarar ne a madadin babban daraktan asusun, domin nuna jin dadinsu ga Gwamna Umar Namadi bisa yadda ya samar wa sabon ofishinsu da aka kafa a yankin na Jigawa.

Aminu Abdu ya kara da cewa, asusun ya horar da ma’aikata a fadin kasar nan, kuma kwalliya na biyan kudin sabulu.

Usman Muhammad Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

Bello Turji ya kashe manoma 11 a Sakkwato

Kasurgumin dan ta’addar nan da ke addabar yankin Sakkwato ta Gabas da Zamfara, Kacalla Bello Turji ya kashe manoma 11 a garin Lugu cikin Karamar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato.

Dan gwagwarmaya da ke biye da lamarin rashin tsaro a yankin Sakkwato ta Gabas Bashiru Altine Guyawa ya sanar wa manema labarai cewa, Turji ya dawo daga yawon sallah ne ya far wa garin da hari.

’Yan bindiga sun kashe mutane 40 a sabon hari a Filato Boko Haram ta kashe mutum 300 ta kwace ƙananan hukumomi 3 a Borno — Ndume

“Turji da yaransa sun bar kauyensa na Fakai a Karamar Hukumar Shinkafi suka shiga wasu kauyukka a Karamar Hukumar Isa a hanyarsu ta komawa Fakai bayan sun gama yawon Sallah suka kashe manoma 11.”

Guyawa yana ganin laifin jami’an tsaro kan lamari, inda suka gaza daukar mataki kan bayanan sirri da suke da shi.

Dan majalisar dokokin jiha, Honarabul Aminu Boza ya ce, ya samu bayanin sai dai dan bindigar bai shiga yankin da yake wakilta ba a lokacin bikin Sallah.

Ya ce, “muna sane da cewa Turji ya shirya kai ziyara a gabashin Gatawa, a nan ne muka dauki mataki, mun je Sabon Birni, inda muka dauki matakin tsaro don kare faruwar hakan, shi ne dalilin huce haushinsa a kan manoma a Isa’’.

Akwai bayanan da ke nuna cewa, Turji ya tsaya a kauyen Tozai, ya kashe shugaban ‘yan sintiri na garin.

A lokacin da aka tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Ahmad Rufa’i ya ce, jami’an soja ne kadai za su iya tabbatar da farmakin saboda su ne ke aiki a yankin.

Duk da sojoji sun ayyana suna neman Turji ruwa jallo, amma ya ci gaba da kai farmaki a kauyukkan gabashin Sakkwato.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran, Iraki Sun Karfafa Dangantakar Makamashi
  • Bello Turji ya kashe manoma 11 a Sakkwato
  • Gwamna Namadi Ya Bada Ai hanyoyi 47 masu nisan kilomita 800 a sassan jihar.
  • Kasashen Larabawa Na Yankin Tekun Farisa Sun Yi Fatan Al-Khairi Ga Iran Da Amurka A Tattaunawar Shirin Nukliyar Kasar
  • Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Siyo Tan Tan 360 Ga Manoma
  • Gwamnatin Amurka Ta Yi Da’war Cewa; Ba Ta Neman Tashin Hankali Tsakaninta Da Iran
  • An sake kama wasu mafarauta ’yan Kano a Jihar Edo
  • A daina cutar ’yan Najeriya ta hanyar rabon kayan tallafi
  • Hajjin 2025: Shirye-shirye Sun Yi Nisa A Jihar Jigawa
  • Za A Samar Da Ababen Hawa Ga Malaman Sakandare A Jigawa