Matsalar “Fentanyl” Ba Laifi Ne Da Amurka Za Ta Iya Dora Wa Wasu Ba
Published: 4th, February 2025 GMT
A kwanan baya, kasar Amurka ta kakaba wa kayayyakin kasar Sin da ake neman shigar da su cikin kasuwanninta karin harajin kwastam na kaso 10%, bisa dalilin wai Sin na sayar da magani mai suna Fentanyl a kasar.
Hakika maganar Fentanyl din wani batu ne da kasar Amurka ta dade tana kokarin ruruta shi, inda wasu ‘yan siyasar kasar ke neman dora laifin yadda mutanen kasar ke amfani da maganin a matsayin miyagun kwayoyi kan kasar Sin, cewa wai “Sin na samar da sinadarin hada maganin Fentanyl, wanda aka sarrafa shi zuwa miyagun kwayoyi a Mexico, tare da kai su cikin Amurka”.
Sai dai a ganin Farfesa Li Haidong na jami’ar diflomasiyya ta Sin, gwamnatin Amurka ta yi sakaci wajen sa ido kan yadda ake amfani da maganin Fentanyl a cikin gidanta, abin da ya sa batun ya zama wata matsalar da ake fuskanta a kasar. Sa’an nan, da gwamnatin kasar Amurka ta ga ta kasa magance matsalar daga tushe, sai ta fara dora laifi ga sauran kasashe da suka hada da Sin da Mexico, don nuna wa jama’arta cewa tana daukar mataki. Ban da haka, ta mai da maganar Fentanyl a matsayin wani dalili na daukar matakin karin haraji kan kayayyakin kasar Sin. (Bello Wang)
এছাড়াও পড়ুন:
Wasu sassan Abuja za su kasance cikin duhu a ƙarshen mako – TCN
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ƙasa (TCN), ya bayyana cewa wasu yankunan Abuja za su fuskanci katsewar wuta a ƙarshen mako saboda aikin gyara da za a yi wa na’urorin lantarki.
A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Juma’a, ya ce ana yin wannan aikin ne na shekara-shekara, kuma za a gudanar da shi a ranakun Asabar da Lahadi.
Zaɓen ƙananan hukumomin Osun na nan daram – Gwamna Adeleke Najeriya ta taɓarɓare bayan mulkin IBB – Peter ObiA sakamakon haka, za a dakatar da wutar lantarki a wasu yankuna na tsawon sa’o’i bakwai a kowace rana.
“Aikin zai gudana daga ƙarfe 9 na safe zuwa 4 na yamma a ranakun biyu,” in ji kakakin TCN, Ndidi Mbah.
Ya bayyana cewa yankunan da za su rasa wuta sun haɗa da Garki Area 1, Asokoro, Apo Legislative Quarters, Apo Resettlement, Gudu, da Apo Mechanic.
Matsalar Wutar Lantarki a NajeriyaNajeriya na fama da matsalar wutar lantarki tun shekaru da dama, duk da cewa ita ce ƙasa mafi yawan jama’a a Afirka da kuma ɗaya daga cikin ƙasashen da ke da arziƙin gas da man fetur.
Rashin wadataccen saka hannun jari a ɓangaren samar da wuta, lalacewar kayan aiki, da satar kayayyakin lantarki sun jawo matsalar wutar ta ƙara muni.
A kowace rana, miliyoyin ’yan Najeriya na fuskantar katsewar wuta ba tare da sanarwa ba, wanda ke shafar kasuwanci, masana’antu, da gidaje.
Hakan ya tilasta wa mutane dogaro da janareto masu amfani da fetur ko gas, wanda ke da tsada kuma yana haddasa hayaƙi mai guba ga muhalli.
Duk da ƙoƙarin gwamnati na inganta fannin lantarki, har yanzu Najeriya na fuskantar matsaloli kamar ƙarancin wutar lantarki da kuma tsadar farashin wuta.
Wannan dalilin ne ya sa mutane da dama ke kiran gwamnati da hukumomin da abin ya shafa da su ɗauki matakan gaggawa don kawo mafita mai ɗorewa.