Wakilin Sin: Dakile Ci Gaban Fasahohin Zamani Ba Zai Yi Tasiri Ba
Published: 4th, February 2025 GMT
Babban wakilin kasar Sin a MDD Fu Cong, ya gudanar da taron manema labarai a hedkwatar MDD dake birnin New York, jiya Litinin bisa agogon birnin, domin gabatar da muhimman tsare-tsare na wa’adin shugabancin kasar Sin a kwamitin sulhu, na wannan wata.
A cewar Fu Cong, a yayin wa’adin shugabancin kwamitin sulhu na MDD a watan nan, kasar Sin za ta mai da hankali kan ra’ayoyin bangarori daban-daban da gudanar da tsarin mulkin duniya, da kula da halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma yanayin da ake ciki a wasu kasashen Afirka.
Da aka tambaye shi game da samfurin kirkirarriyar basira ta DeepSeek, wanda wani kamfanin kula da fasahohin kirkirarriyar basira na kasar Sin ya fitar, Fu Cong ya jaddada cewa, kada a raina hazakar masu binciken kimiyya da fasaha na kasar Sin, domin DeepSeek ya jawo hankulan mutane a duniya, kuma ya sa wasu mutane cikin damuwa da tsoro, wanda ke nuna cewa, dakile fasahohi ba zai yi tasiri ba, kana wannan darasi ne da ya kamata kasashen duniya, musamman ma Amurka, su koya.(Safiyah Ma)
এছাড়াও পড়ুন:
Yaya ‘Yan Siyasar Amurka Ke Kasafta Harajin Ramuwar Gayya?
Manufar “ramuwar gayya” ba za ta daidaita gibin cinikin da kasar Amurka take fuskanta ba, illa ta daga farashin kayan da ake shigarwa kasar daga kasashen waje, da haddasa hadarin hauhawar farashin kaya a kasar, da kawo illa ga zaman rayuwar jama’ar kasar. A karshe Amurka ba za ta cimma burinta na zama a matsayin koli a duniya ba. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp