Shugaban Majalisar Wakilai Dr Abbas Tajuddeen, ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar fitaccen dan kasuwa kuma mai taimakon jama’a, Alhaji Bala Abdulwahab da ke Zariya, wanda aka fi sani da Albabello.

A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Malam Musa Abdullahi Krishi ya fitar, Dakta Abbas Tajuddeen, ya ce masarautar Zazzau da jihar Kaduna sun yi rashin babban dan kasuwa wanda ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya wajen yi wa al’umma hidima.

Shugaban majalisar ya jaddada cewa, Albabello, ta hanyar sahihancinsa na kasuwanci, ya samar da ayyukan yi ga dubban jama’a a Zariya da ma fadin kasar nan, ta hanyar amfani da rassan kamfaninsa daban-daban.

Ya ci gaba da cewa Albabello, ya kuma gina makarantun firamare da sakandare da dama don inganta ilimi;  da masallatai, domin ci gaban al’umma.

Hakazalika, a yayin rayuwarsa marigayin ya  dauki nauyin bayar da tallafin karatu ga dalibai don yin karatu a Najeriya da kasashen waje, da sauransu.

Dr Tajuddeen, ya yi addu’a ga  Allah SWT dayYa ji kan marigayi Alhaji Bala Abdulwahab, Ya kuma bai wa iyalansa hakurin jure rashin.

Alhaji Bala Abdulwahab, wanda shi ne wanda ya assasa kamfanin Albabello Trading Company Limited da ke Zariya, ya rasu ne a ranar Litinin 3 ga watan Fabrairun 2025, yana da shekaru 68.

Daga Salihu Tsibiri

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Rasuwa Shugaban Majalisar Wakilai

এছাড়াও পড়ুন:

HOTUNA: Zulum ya karɓi baƙuncin Majalisar Sarakunan Arewa a Borno

Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya karɓi baƙuncin Majalisar Sarakunan gargajiya ta Arewa a wani taronta karo na bakwai da ta gudanar a ranar Talata.

Taron wanda ya gudana a birnin Maiduguri, an yi shi ne domin lalubo hanyoyin ƙarfafa tsaro da haɓaka ci gaban yankin.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Kaduna ta Amince da Kudirin Kula da Lafiyar Kwakwalwa na Jihar
  • Al’ummar Babura Sun Karrama Sabon Shugaban Asibitin Koyarwa Na Rasheed Shekoni
  • HOTUNA: Zulum ya karɓi baƙuncin Majalisar Sarakunan Arewa a Borno
  • Sabon Shugaban Kasar Gabon Ya Bayyana Shiransa Na Kawo Sauyi Mai Kyau A kasar
  • ‘Yansanda Sun Kama Wani Kato Bisa Zargin Cin Zarafin Wata Mata A Adamawa
  • ’Yar shekara 66 ta haifi ɗanta na 10 da kanta
  • Shugaban Kasar Iran Ya Mika Ta’aziyyar Ta Rasuwar Wanda Ya Assasa Hukumar  Makamashin Nukiliya Ta Iran
  • Sojojin Yemen Sun Kakkabo Jirgin Yakin Amurka Wanda Ake Sarrafa Shi Daga Nesa Na 19
  • ’Yan adawa sun zama kyanwar Lami duk da rinjayensu a Majalisa
  • Ta kai ƙarar kamfanin jirgi da fasinja kan kukan yaro