‘Yan Sanda Sun Mika Bakin Haure 165 Ga Hukumar Shige Da Fice Ta Kasa
Published: 5th, February 2025 GMT
Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Kebbi, ta kama wasu bakin haure 165 tare da mika su ga hukumar kula da shige da fice ta kasa shiyar jihar domin gudanar da bincike.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar ya fitar kuma ya mikawa gidan rediyon Najeriya a jihar Kebbi, ya ce, bisa rahoton bayanan sirri, an gano sama da mutum dari biyu a wani katafaren gida mai dakuna uku da ke unguwar Kuwait a cikin birnin Birnin Kebbi.
Sanarwar ta ce, tawagar jami’an ‘yan sanda da ke sashin binciken manyan laifuka (SCID) ce ta kai samame unguwar, inda suka yi nasarar cafke mutane dari da sittin da biyar (165).
Ya bayyana cewa, yayin da ake gudanar da bincike, an gano cewa, dukkan wadanda ake zargin sun fito ne daga kasashen Faransa da suka hada da Burkina Faso, da Jamhuriyar Benin, da Jamhuriyar Nijar, da Mali da Ivory Coast.
A cewar sanarwar, bincike ya kara nuna cewa, wadanda ake zargin suna zaune ne a Najeriya ba tare da wasu takardu masu inganci ba.
Sanarwar ta ce, bayan kammala binciken farko da rundunar ta gudanar, an mika wadanda ake zargin zuwa hukumar kula da shige da fice ta kasa shiyyar jihar Kebbi, domin ci gaba da bincike da kuma daukar matakin da ya dace.
Daga Abdullahi Tukur
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Hukumar Kula da Shige da Fice
এছাড়াও পড়ুন:
Kakakin ’yan sandan Taraba, Abdullahi Usman, ya rasu
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba, SP Abdulahi Usman, ya rasu bayan fama da doguwar jinya.
Kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ne, ya tabbatar da rasuwarsa cikin wata sanarwa a ranar Laraba.
’Yan fashi 4 sun mutu yayin tsere wa ’yan sanda a Nasarawa Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadagoYa bayyana Usman a matsayin jajirtaccen ɗan sanda kuma gada tsakanin jami’an tsaro da al’umma.
“SP Usman ya shafe shekaru uku yana ƙarfafa hulɗa tsakanin ’yan sanda da jama’ar Taraba.
“Ƙwarewarsa, mutuntaka da jajircewarsa wajen neman adalci sun an samu tasiri,” in ji Adejobi.
Ya ƙara da cewa rasuwar Usman babban rashi ne ga rundunar ’yan sanda, abokan aikinsa da duk wanda ya san shi.
Sashen hulɗa da jama’a na ’yan sanda ya miƙa ta’aziyya ga iyalansa da kuma ‘yan uwansa, tare da yin addu’ar Allah Ya masa rahama.
Za a ci gaba da tunawa da Usman saboda sadaukarwar a aikinsa da ƙoƙarinsa na kyautata hulɗa tsakanin ’yan sanda da al’umma a Jihar Taraba.