Masana Kimiyyar Sin Sun Kirkiro Sabuwar Fasahar AI Mai Hasashen Zuwan Mahaukaciyar Guguwa
Published: 5th, February 2025 GMT
Masana kimiyyar kasar Sin sun kirkiro wani sabon samfurin kirkirarriyar basira ta fasahar AI domin yin hasashen zuwan mahaukaciyar guguwa, wanda hakan ya ba da sabuwar fa’ida da kara haskaka hanyoyin inganta shirin tunkarar bala’o’i a duniya.
A kwanan baya, masu bincike daga cibiyar nazarin teku a kwalejin kimiyya ta kasar Sin sun wallafa wannan binciken a cikin mujallar da ke wallafa harkokin kimiyya ta kasar Amurka, watau “Proceedings of the National Academy of Sciences.
এছাড়াও পড়ুন:
Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Karfafa Gwiwar Kamfanonin Kasashen Duniya Da Su Fadada Zuba Jari A Sin
Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng ya bayyana a jiya Lahadi cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen waje, kuma tana maraba da kamfanonin kasashen duniya da su fadada zuba jari a kasar Sin, domin zurfafa samun moriyar juna da samun nasara tare.
He ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da shugabannin manyan kamfanoni na duniya a nan birnin Beijing, yayin da suka yi musayar ra’ayi kan yanayin tattalin arzikin duniya da na kasar Sin, da hadin gwiwar Sin da Amurka a fannin tattalin arziki da cinikayya, da fadada zuba jari a kasar Sin.
He ya ce, tattalin arzikin kasar Sin yana da karfin juriya, da fa’ida mai yawa, da wadataccen kuzari, ya kara da cewa, kasar Sin ta kuduri aniyar samun ci gaba mai inganci, da fadada bude kofa ga kasashen waje a babban mataki, da ci gaba da kyautata yanayin kasuwanci, tare da maraba da kara zuba jari da kamfanonin kasa da kasa suke yi a kasar Sin, don cin gajiyar damammakin da ke tattare da ci gaban kasar.
Shugabannin harkokin kasuwanci na kamfanoni na kasa da kasa da suka halarci wannan taro sun bayyana cewa, suna dora muhimmanci kan kasuwar kasar Sin, kuma suna da kwarin gwiwa game da makomar tattalin arzikin kasar Sin, kana sun bayyana aniyarsu ta yin hadin gwiwa na dogon lokaci tare da kasar Sin. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp