Masu Fama Da Cutar Daji Sun Bukaci Gwamnatin Kano Basu Tallafi
Published: 5th, February 2025 GMT
Kungiyar masu fama da cutar daji ta Najeriya reshen jihar Kano, ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta bullo da tallafin kula da cutar a dukkan asibitocin gwamnati.
Shugaban kungiyar Salisu Yusuf ne ya yi wannan kira a yayin wani taron manema labarai na bikin ranar cutar Daji ta duniya tta shekarar 025.
Ya bukaci gwamnati da ta hada gwajin cutar Kansa, da jiyya, da kula da lafiyar jiki a cikin shirinta na ba da tallafin iwon lafiya.
Acewarsa matakin zai rage wa majinyata matsalar kudi, musamman wadanda suka fito daga iyalai masu karamin karfi.
Bugu da kari, kungiyar ta bukaci da a saka masu fama da cutar ta Daji da wadanda suka warke daga cutar a cikin shirin nan na Abba Care da aka kaddamar kwanan nan, wanda ke da nufin tallafa wa mutane masu raunu su 300,000.
Salisu Yusuf ya jaddada cewa cutar Kansa ta kasance babbar lalurar da ke bukatar kulawa cikin gaggawa. “Yawancin mutane na kokawa dangane da biyan kuɗin tantance masu dauke da cutar, da kudaden cigaba da samun kula da karbar magani idan aka gano suna dauke da cutar.
Kungiyar ta masu fama da cutar daji ta Najeriya ta yabawa kokarin gwamnatin jihar na inganta fannin kiwon lafiya, tare da yin kira ga masu hannu da shuni, da kungiyoyi masu zaman kansu, da cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu, da su tallafawa shirin kula da cutar Daji a Kano.
Ta jaddada kudirinta na bayar da shawarwarin sauye-sauyen tsarin da ke ba masu fama da cutar Kansa fifiko a Kano, ta hanyar wayar da kan jama’a da shirye-shiryen gano cutar da wuri.
Taken ranar Ciwon Daji ta Duniya na 2025, “United by Unique,” yana nuna mahimmancin aikin gamayya wajen yaƙar cutar Kansa.
Abdullahi Jalaluddeen
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Ranar Cutar Daji Ta Duniya masu fama da cutar da cutar Daji cutar Kansa da cutar da
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Na Maraba Da Masu Zuba Jari Domin Su More Damammakin Bunkasarta
Dadin dadawa, Sin za ta ci gaba da shimfida yanayin ciniki mai inganci, da samarwa kamfanonin ingantattun hidimomi. Sin na maraba da masu zuba jari na sassan duniya da su gudanar da hada-hadarsu a kasar musamman ma wannan tasha ta ciniki maras shinge da more zarafin ci gaban Sin tare. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp