Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-04-14@20:51:47 GMT

An Kara Wa’adin Yin Rajistan Aikin Hajjin 2025

Published: 5th, February 2025 GMT

An Kara Wa’adin Yin Rajistan Aikin Hajjin 2025

Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON ta sanar da a ci gaba da yi wa maniyyata rajista har zuwa ranar Litinin 10 ga watan Fabrairu, 2025.

A daren Talata 4 ga watan ne  hukumar ta amince da kara lokacin  a taron da ta yi da shugabannin hukumomin alhazai na jihohi.

Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na  hukumar Jin Dadin Alhazzai ta Jihar Kaduna  Yunusa Mohammed Abdullahi ya fitar, ya ce shugaban hukumar Malam Salihu S.

Abubakar ya yi kira ga maniyyatan jihar ta Kaduna da su yi amfani da wannan damar wajen yin rajista ta hanyar tuntubar jami’anmu da ke kananan hukumomi don su cika kudadensu, ko karbar sabuwar telar banki don su biya kafin a rufe.

Ya ce wannan ita ce dama ta ƙarshe da suka nema a wajen taron da suka yi da NAHCON.

Kudin kujera a bana dai ya kama Naira miliyan takwas da dubu dari hudu da hamsin da biyar,  da dari shida da tamanin da biyar,  da kobo hamsin da tara(8, 457, 685.59).

Safiyah Abdulkadir

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Wa adin Rajista

এছাড়াও পড়ুন:

Kashe-kashen Filato: Jami’an tsaro na sassauta wa masu laifi —Tsohon gwamnan soji

Jami’an tsaro Gwamnatin Tarayya suna sassauta wa masu kashe mutane babu gaira babu dalili a Jihar Filato, a cewar tsohon jihar na mulkin soji, Rear Admiral Samuel Bitrus Atukum.

Da yake tsokaci kan kisan gillar da ka yi wa mutane 52 tare da lalata kadarori na miliyoyin naira baya-bayan nan a yankin Ƙaramar Hukumar Bokkos, Atukum ya ce, “Ina da matsala kan yadda jami’an tsaro ke tunkarar matsalar. A gani na suna sassauta musu. Mene ne abu mai wahala a ba wa sojoji umarni su je maɓoyar masu wannan aika-aika su kamo su?

“Daga kan tsaunuka mutanen nan suke saukowa ɗauke da makamai su halaka jama’a, sannan su ɓace, kuma a nan suke ɓoye makamansu. Saboda haka ya kamata jami’an tsaro su yi fiye da  abin da suke yi yanzu.

“Kamata ya yi a ayyana waɗannan mutane a matsayin ’yan ta’adda, saboda ta’addanci suke yi, amma an kasa, sai a je ana kama masu ƙananan laifi da sunan manyan laifuka,” in ji Atukum wanda shi ne gwamnan Filato daga 1984 zuwa 1985.

Mahaifi ya yi wa ’yarsa ciki a Bauchi An gano gawar makiyayi da ƙwato shanu a Filato Mutane 300 sun kamu da cutar sanƙarau Sakkwato

Ya bayyana cewa a lokacin da yake gwamna rikicin addini na ƙungiyar Maitatsine ya ɓarke, amma cikin ɗan ƙanƙanin lokaci aka murƙushe shi, saboda gwamnati ta tari matsalar tun daga tushe kafin a je ko’ina.

Ya ce idan za a ɗauki irin matakin daga sama a kan matsalar tsaron Filato, shugaban ƙasa ya ba wa jami’an tsaro umarni a matsayinsa na Babban Kwamandan Tsaron Ƙasa, za su yi abin da ya kamata.

“Amma ba a ba da umarni ko ɗaukar mataki ba, sai mutane sun yi ta ƙorafi kan matakin da gwamnati ta ɗauka, sai a fito ana cewa za a kamo waɗanda suka aikata abin, a hukunta su daidai da abin da doka ta tanada. Wannan shi ne abin da muke ta ji.”

Ya ce, “Da ni ke da iko, da umarni da wa’adi ƙarara zan na wa jami’an tsaro cewa ga abin da nake so. Idan shugaban ƙasa da gaske yake kan matsalar tsaro, umarni kawai zai bayar kuma yana da tasiri a kan Majalisar Dokoki ta Ƙasa, duk abin da yake so za ta yi aiki a kai, kuma a tafi tare da ɗaukacin al’ummar ƙasa.

“Amma ya za a yi ka ce kana maganin abun, amma ba a ga alamar komai ba? Wa zai ɗauka da gaske kake, alhali ba a ga an kamo masu aikata laifin an hukunta su ba?

“A wannan yanayi da matsala ke fama da matsalar rashin aiki, mutane za su yi ta amfani da irin wannan giɓi wajen yin irin waɗannan aika-aika da muke gani.

“Har ta kai ga masu yin wannan ta’asa na ba da umarnin cewa ga wanda suke so a naɗa a matsayin shugaɓan wata hukumar tsaro, ko kuma a sauke wanda yake kai,” in ji tsohon gwamnan sojin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaba Tinubu Ya Yi Allah-wadai Da Harin Jihar Filato
  • Tsangayar Ilimi Ta BUK Ta Yi Bikin Cika Shekaru 50 Da Kafuwa
  • Aljeriya ta yi barazanar korar jami’an diflomasiyyar Faransa 12
  • Shugaban Kasar Iran Ya Mika Ta’aziyyar Ta Rasuwar Wanda Ya Assasa Hukumar  Makamashin Nukiliya Ta Iran
  • Tinubu Ya Kaddamar Da Ci Gaba Da Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna 
  • Hajjin 2025: Shirye-shirye Sun Yi Nisa A Jihar Jigawa
  • Sama da mutane 1,560 ne sukayi shahada tun bayan da Isra’ila ta koma kai farmaki Gaza
  • MDD: Mafi Yawancin Wadanda Yaki Ya Ci A Gaza Mata Ne Da Kananan Yara
  • Kashe-kashen Filato: Jami’an tsaro na sassauta wa masu laifi —Tsohon gwamnan soji
  • Dalilin Nijeriya Na Karbo Bashin Dala Biliyan 12 Daga Kasar Japan