Amnesty Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Kama Benjamin Netanyahu
Published: 5th, February 2025 GMT
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty International” ta kira yi Amurka da ta kama Fira ministan “Isra’ila” Benjamin Netanyahu da yake ziyarar aiki a kasar.
A wasu jerin sakwanni da kungiyar ta kare hakkin bil’adama ta duniya ta wallafa a shafinta na X, ta bayyana cewa; Yadda Amurka ta karbi bakuncin Benjamin Netanyahu alhali ana zarginsa da manyan laifuka, yana nuni da cewa ta raina kotun ta kasa da kasa.
Har ila yau kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ta kuma kara da cewa; Gwamnatin da ta gabata ta Amurka a karkashin Joe Biden ta yi watsi da duk wani yunkuri na shimfida adalci a duniya, kuma shi ma shugaba Trump abinda yake yi kenan a yanzu.
Wannan ce ziyara ta farko da Fira ministan HKI Benjamin Netanyahu ya kai zuwa waje, tun bayan da kotun kasa da kasar ta fitar da sammacin kamo shi, saboda aikata manyan laifuka da su ka hada da kisan kiyashi.
A ranar 21 ga watan Nuwamba 2024 ne dai kotun kasa da kasa ta fitar da sammacin a kamo Benjamin Netanyahu da ministansa na yaki Yoav Gallant, saboda laifukan da su ka tafka a Gaza.
A karshe kungiyar kare hakkin bil’adaman ta ce, bai kamata ba a bai wa masu aikata laifukan yaki akan bil’adama mafaka.”
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kare hakkin bil adama Benjamin Netanyahu
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yansanda Sun Kama Wani Kato Bisa Zargin Cin Zarafin Wata Mata A Adamawa
Rundunar ‘Yansandan Jihar Adamawa ta kama Umar Shaibu bisa zargin cin zarafin wata mata a yankin Jimeta a jihar. An kama Shaibu ne bayan wani bidiyo mai tayar da hankali ya yadu a kafafen sada zumunta, kamar yadda Jami’in hulda da Jama’a na ‘Yansandan Jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje, ya bayyana. Salamatu Yakubu, matar mai shekaru 22 daga Angwan Tana, an ce wanda ake zargin ya yi ma ta dukan jakin ne mai tsanani, Shaibu, wanda ake cewa shi ne dan uwanta.
Wannan lamarin ya janyo zarge-zargen daga al’umma da kuma kiran da aka yi wa Yansanda daga mutanen gari, da kungiyoyin fararen hula, da sauran masu rajin kare hakkin bil’adama domin a kama wanda ake zargi.
Ƴansanda Sun Kama Ɓarayin Waya Masu Amfani Da Keke Napep A Adamawa An Kama Wanda Ake Zargi Da Kashe Mai PoS A AdamawaAn kama Shaibu ne tare da taimakon al’umma ta hanyar dabarun kula da tsaro na cikin gari. An tura matar da aka yi wa dukan cutar zuwa asibiti domin samun kulawar likita.
A halin yanzu, wanda ake zargin yana tsare a sashin binciken laifuka na musamman na Jihar (SCID) a sashin kula da mata domin a gudanar da cikakken bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kotu. Rundunar Yansandan ta tabbatar wa da jama’a cewa za a binciki lamarin sosai kuma wanda ake zargi zai fuskanci shari’a bisa dokokin da suka dace.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp