An soma rigimar haraji tsakanin China da Amurka
Published: 5th, February 2025 GMT
A bayan nan ne Amurka ta sanya harajin kashi 25 a kan kayayyakin da ake shigar wa ƙasar daga Canada da Mexico da kuma kashi 10 kan kayayyakin makamashi na Canada, yayin da kayayyakin China za su fuskanci harajin kashi 10.
Sakatariyar yaɗa labaran Fadar White House, Karoline Leavitt, ce ta bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai a ranar Juma’a.
Ta bayyana cewa “Canada da Mexico suna ba da damar shigar da muguwar ƙwayar nan ta fentanyl da ke kashe Amurkawa da kuma baƙin haure ba bisa ka’ida ba zuwa kasar mu.”
Ta ce Shugaba Donald Trump ya ba da umarnin wanda zai soma aiki daga ranar Talata, domin magance matsalar shigar da maganin kashe raɗaɗi na fentanyl da matsalar ‘yan gudun hijira da ke shiga Amurka ba bisa ƙa’ida ba.
“Shugaba Donald Trump na ɗaukar ƙwararan matakai don kare Amurkawa daga matsalar maganin na fentanyl. Fentanyl shi ne kan gaba wajen sanadin mutuwar Amurkawa masu shekaru 18 zuwa 45,” in ji Leavitt.
Amurkan dai ta zargi masu safarar miyagun ƙwayoyi na Mexico da kasancewa “kan gaba a duniya wajen safarar” fentanyl da sauran ƙwayoyi, yana zargin akwai ƙawance tsakanin masu safarar da gwamnatin Mexico.
Game da Canada, Fadar White House ta yi ƙarin haske game da ƙaruwar samar da maganin na kashe raɗaɗi na fentanyl da kuma tsallaka wa da shi kan iyaka ba bisa ƙa’ida ba, tana mai cewa: “an kama fentanyl a kan iyakar Arewa a bara wanda zai iya kashe Amurkawa miliyan 9.8.”
An soki China saboda zargin tana taka rawa wajen bayar da tallafi ga kamfanonin sinadarai wajen fitar da fentanyl zuwa ƙasashen waje, inda Fadar White House ta yi iƙirarin cewa: “ba wai kawai China ta gaza wajen daƙile tushen haramtattun ƙwayoyi ba, har ma tana taimaka wa wannan kasuwanci.”
Martanin Canada da Mexico
Ƙasashen Canada da Mexico sun sanar da ɗaukar matakan ramuwar gayya kan harajin da Shugaba Trump ya ɗora wa kayayyakinsu.
A ranar Asabar, Firaminista Justin Trudeau ya ce Canada za ta sanya harajin kashi 25 kan kayayyakin Amurka da suka kai dala biliyan 106.5 a matsayin martani ga harajin Amurka.
Harajin dala biliyan 20 zai fara aiki daga ranar Talata, sannan na dala biliyan 86 zai fara aiki a cikin kwanaki 21, kamar yadda Trudeau ya shaida wa wani taron manema labarai.
Trudeau ya yi gargaɗin cewa harajin zai cutar da Amurka, wacce daɗaɗɗiyar ƙawar ƙasar ta Canada ce.
Ya nemi mutanen Canada su riƙa sayen kayayyakin da aka yi a ƙasar, kuma su riƙa gudanar da hutu a gida maimakon a Amurka.
Ya ce ana kuma duba wasu matakan da ba na haraji ba, da suka haɗa da wasu da suka shafi ma’adanai masu mahimmanci da sayen makamashi da sauran ɓangarorin haɗin gwiwa.
Trudeau ya kuma ƙara da cewa, ƙasashen Canada da Mexico suna aiki tare don fuskantar harajin da Washington ta ɗora wa kayayyakinsu.
Fadar White House ta ce manufar harajin ita ce matsa wa Mexico da Canada da China lamba su ƙara ba da haɗin kai kan daƙile shigar da miyagun ƙwayoyi da tsaron kan iyakoki da hana kwarar baƙin haure shiga ƙasar ta ɓarauniyar hanya.
China ta bi sahu
China a wani mataki na ramuwar gayya ta lafta wa Amurka harajin kaso 15 cikin 100 na kayayakin kwal da na makamashin gas da ake shigar da shi kasar daga Amurka.
Ƙarin harajin a cewar Ma’aikatar Kuɗin Beijing zai fara aiki ne a makon gobe.
A cikin sanarwar da ta fitar ta ɗaukar matakan ramuwa, China ta zargi Amurka a ƙarƙashin Donald Trump da karya ƙa’idojin kasuwanci na ƙasa da ƙasa.
“Gaban kai da Amurka ta yi ita kaɗai ta lafta haraji ya saɓa ƙa’idojin Hukumar Kasuwaci ta Duniya. Wannan ya saɓa wa yarjeniyoyin kasuwanci da tattalin arziƙi tsakanin China da Amurka.”
Bugu da ƙari China ta sanar matakin fara bincike a kan kamfanin fasaha na Google.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Fadar White House
এছাড়াও পড়ুন:
Sharhi: Tattaunawa Zagaye Na Farko Tsakanin Iran Da Amurka A Oman
Sharhin zai yi dubi ne game da tattaunawar da aka fara gudanarwa zagaye na na farko tsakanin Iran da Amurka a birnin Mascut fadar mulkin kasar Oman, inda gwamnatin kasar Oman din take shiga tsakani a wannan tattaunawa wadda aka fara gudanarwa.
Tun da safiyar Asabar ne dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya isa birnin Mascut na kasar Oman da can ne za a yi tattaunawar da ba ta gaba da gaba ba a tsakanin jamhuriyar musulunci da Amurka.
Jim kadan bayan isar tasa birnin Mascut ministan harkokin wajen na jamhuriyar musulunci ta Iran ya gana da mai masaukinsa Sayyid Badar al-Busa’idi,inda ya mika masa takardu akan mahangar Iran.
A yayin ganawar da bangarorin biyu su ka yi, ministan harkokin wajen Iran ya yaba da matsayar Oman akan batutuwa da dama su ka shafi wannan yankin na yammacin Asiya.
Daga cikin masu yi wa ministan harkokin wajen na Iran rakiya da akwai mataimakinsa a fagen dokokin kasa da kasa Kazim Garib Abadi, kamar yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Isma’ila Baka’i ya ambata.
Iran da Amurka suna tattaunawa ne ta hanyar shiga tsakanin kasar Oman ba ta gaba da gaba.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baqaei ya bayyana cewa, kwana guda gabanin tattaunawar a kasar Oman tsakanin Amurka da Iran kan shirin nukiliyar kasar Iran, akwai damammaki da dama na diflomasiyya da Amurka za ta iya tabbatar da aniyarta a kansu
Baqaei ya rubuta a dandalin X cewa, “Ya kamata Amurka ta mutunta wannan shawarar da aka yanke duk da cewa ana fama da rikici.”
“Ba za mu yanke hukunci ba, Muna da niyyar tantance niyyar dayan bangaren kuma za mu tabbatar da hakan a wannan tattaunawa,” in ji jami’in diflomasiyyar na Iran, ya kara da cewa Iran “za ta yi tunani kuma ta mayar da martani ga kowane mtaki.”
A ranar Litinin din makon da ya gabata ne shugaban Amurka Donald Trump ya ba da sanarwar cewa gwamnatinsa za ta shiga tattaunawa da Iran.
Kafin zuwa ga wannan tattaunawar dai bangarorin biyu sun yi musayar kalamai masu zafi, inda Trump ya yi barazanar daukar matakin soji idan tattaunawar ta ci tura.
Dangane da gargadin na Trump, wani babban mataimaki ga jagoran Iran Ayatollah Sayyed Ali Khamenei ya ce Iran za ta iya daukar dukkanin matakan da ta ga sun dace a kan wannan lamari.
Ganawar ta ranar Asabar na zuwa ne biyo bayan wata wasika da Trump ya aikewa Sayyed Khamenei a watan da ya gabata, inda ya bukaci Tehran da ta shiga tattaunawa, tare da yin gargadin cewa matakin soji na kan teburi idan Iran ta ki amincewa.
Tehran ta bayyana aniyar ta na shiga tattaunawar kai tsaye amma muddin Washington ta ci gaba da aiwatar da manufofinta na matsin lamba mafi tsanani a kan Iran, to kuwa tabbas wannan tattaunawa ba za ta iya haifar da da mai ido ba.
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya ce Amurka na da masaniya kan irin karfin kare kai da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke da shi, yayin da ya ce kasar ta shirya tsaf domin kare kanta.
Ya kuma jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta yarda da Washington ba, amma duk da haka za ta gwada ta yayin tattaunawar,” in ji Abbas Araghchi.
Babban jami’in diflomasiyyar ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta neman yaki, amma idan ya zama dole ta san yadda za ta kare kanta. »
“Muna da shaku kan aniyar Amurka kuma ba mu da tabbacin cewa suna da niyyar gudanar da tattaunawa ta gaske, amma za mu gwada su.”
Haka nan kuma jami’in diflomasiyyar na Iran ya yi watsi da zargin kasashen yamma – karkashin jagorancin Washington – cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran na neman mallakar makamin nukiliya.
Ya ce zargin da ake yi wa Iran na neman mallakar makamin nukiliya, zargi ne mara tushe balantana makama.
Dangane da bayanan da aka yi ta yadawa musamman daga bangaren mahukuntan Amurka na cewa tattaunawar za ta gudana ne tsakanin Iran da Amurka gaba da gaba, Araghchi ya bayyana imaninsa cewa irin matakan da Iran ta dauka a baya-bayan nan dangane da wannan tattaunawa wani babban yunkuri ne na diplomasiyya.
Ya fayyace cewa sabanin wasu fassarori da aka yi a baya-bayan nan a game da batun tattaunawa tsakanin kasashen biyu, inda ya ce kokarin bayyana ra’ayi ne na gaskiya da bude hanyar diflomasiyya.
Dangane da kalaman Trump da ya yi a ranar litinin, Araghchi ya bayyana cewa Iran a shirye take domin ganin an cimma matsaya, inda za ta halarci tattaunawa a kasar Oman a ranar Asabar.
Ya kuma kara da cewa, wannan ba sabon lamari ba ne, domin ita kanta Amurka tana tsakiyar yin shawarwari kai tsaye game da batun Rasha da Ukraine, batun da ya fi zafi da sarkakiya ta fuskar siyasa da tattalin arziki a mataki na kasa da kasa.