‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 2 A Dajin Bauchi
Published: 5th, February 2025 GMT
Jami’an ‘yansanda tare da hadin gwiwar mafarauta sun kashe wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne a Dajin-madan, da ke karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi. Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu a safiyar ranar Laraba, Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Bauchi, CSP Ahmed Wakil, ya ce an kashe ‘yan bindigar ne ta hanyar amfani da bayanan sirri da hadin gwiwa da masu sa ido da ke cikin al’ummomin da abin ya shafa.
এছাড়াও পড়ুন:
Harin ’Yan bindiga: Mun yi asarar shanu sama da miliyan 4 – Miyetti Allah
Ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) ta yi iƙirarin cewa wasu ’yan bindiga sun sace sama da shanu miliyan huɗu na mambobinta musamman a yankin Arewa maso Yamma.
Shugaban Ƙungiyar MACBAN na ƙasa, Baba Usman ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da sababbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙungiyar na jiha a Jihar Kebbi.
’Yan bindiga sun kashe mutum 12, sun sace wasu a Zariya Hisbah ta rufe gidajen rawa a KatsinaYa ce, ɓarayin shanu na yawan kai wa Fulani makiyaya hari, lamarin da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.
Usman ya jaddada cewa, ana yawan sauya fahimtar Fulani makiyaya da kuma yin kuskuren sanya su a matsayin masu tayar da fitina, inda ya buƙaci jama’a su riƙa ganin su a matsayin ’yan Najeriya masu son zaman lafiya.
Ya kuma yi kira ga makiyaya da su guji shiga gonaki, su kuma zauna lafiya da manoma domin hana rikice-rikice.
Usman ya kuma yabawa gwamnatin tarayya da na jihohi bisa kafa ma’aikatar kiwo, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen magance matsalolin da makiyaya ke fuskanta.
Ya kuma yabawa gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris bisa ayyukan da suka inganta rayuwar al’ummar Fulani.