HausaTv:
2025-02-21@14:53:00 GMT

Kissoshin Rayuwa Sirar Imam Hassan (a) 12

Published: 5th, February 2025 GMT

12-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa Shirin wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane rastan na shahid Aya. Murtadha muttahhari, ko cikin littafin Mathnawi na maulana jalaluddeen ,Rumi, ko kuma cikin wasu littafan.

Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Alhassan (s) Jikan manzon All..(s) sannan limami na 2 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s) kuma da na farko ga  Fitima(s) diyar manzon All..(s).

Kuma a cikin shirimmu da ya gabata mun yi maganar yadda manzon All..(s), bayan kwanaki kadan da komawarsa Madina daga aikin Hajji, sai All..ya umurce shi ya je makabartar Bakiyya, ya kuma nemam masu gafara, don haka a cikin dare ya kira, daya daga cikin yentattun bayinsa wanda ake kira Abu Maubihah inda ya fada masa cewa, an umurce ni in nemawwa mutanen makabartan bakiyya gafara daga All ..T kuma ina son ka rakani.

A lokacinda suka isa makabartar sai ya fadawa Abu Maubihah, kan cewa an bani zabi na mubudan taskokin duniya har abada, sannan aljanna, da kuma haduwa da All..,na a yanzu,  amma na zabi haduwa da Ubangiji na All…

Sai kuma bayan kwanaki kadan, manzon All..(s) sai fara rashin lafiyarsa ta karshe, Sannan ya fara tunanin yadda iko zai koma ga Aliyu dan Abitalib (a) a bayansa ba tare da wata matsala ba. Ya so ya dauki wadannan matakan ne, saboda ya fahinci cewa akwai wasu manya-manyan sahabban manzon All..(s) wadanda suke kodayin shugabaci a bayansa.

Don haka ne ya tada rundunar Usama dan Zaidu, dan shekara 17 a duniya, sannan tattara dukkan wadannan manya-manyan sahabbansa, daga cikin muhajirun da ansar, tare da Umurnin su tafi yaki zuwa kasar Ruma ta gabas don yaki da su. Don haka, kafin su dawo yayi wafati, sannan Aliyu dan Abitalib ya karbi shugabanci ba tare da wata matsala ba. Kuma ko sun dawo ba zasu iya yi masa tawaye ba.

Manzon All..ya nunawa Usama dukkan dabarbarun yakin da yaki bukata. Sannan ya bashi tutar, ya ce masa ya kama hanya. Sai Usama ya  je wani wuri a bayan madina wanda ake kira Jurf ya kafa sansanin sojojinsa yana jiransu  su fita.

Usama yayi ta jiransu, amma suka ki fitowa, wasu ma suka fara sukar shugabancin Usama dan Zaidu, a wannan yakin. A lokacinda labari ya zo masa, cewa wasu sunki fita, sannan sun fara sukansa kan shugabantar da Usama, a nan ma sai ya sake fitowa, ya yi masu Magana inda ya sake jaddada masu cewa, Usman ya canacanci shugabanci, haka ma babansa kafin shi. Duk da cewa a lokacimma sun ki amincewa da jagorancin bababansa.

Mun kama fara kawo maku darussan da za mu iya dauka, a cikin wannan hadisin, na cewa dabarar da manzon All..(s) ya yi na nisantar da masu kodayin mulki a bayansa ya kasa samun nasara. Amma kuma ya zama hujja a kansu har duniya ta nade.

sannan su ma sun fahinci haka, shi ya sa suka sabawa manzon All..(s). Bayan haka

mun ji cewa a cikin manya-manyan sahabban da ya Sanya a cikin rundunar Usama akwai, Abubakar, da Umar da Abu ubaida dan Jarrah da Usman da sauransu.

Sanna ya ki sanya su kan rundunar ne, don kada wani daga cikinsu ya yi amfani da matsayin don su maida shi damar biyar bukatunsu na kaiwa da shugabanci a bayansa.

Don haka ya tushe masu hanya, sannan ya la’anci duk wanda ya ki tafiya da rundunar Usama.

Banda haka wa ta dubarar da manzon All..(s) ya yi, na shugabantar da Usama dan Zaidu kan wadannan manya-manyan sahabban, shi ne ya nuna masu cewa, shugabanci cancanta ce, ba yawan shekaru ba.

Kuma All..ya na bawa shugabanci ne, ga wadanda ya ga dama, kuma zai bashi ilmi da kuma karfin da yake bukata don cancantar shugabancin.

Don haka manzon All..(s) ya bar wannan duniyar, manya-manyan sahabban manzon All..(s) suna, karkashin shugabancin Usama dan Zaidu wanda bai fi shekaru 17 a diniya ba.

A wani hadisi manzon All..(s) ya na cewa: wanda ya gabatar da kansa a cikin musulmi al-hali ya san cewa akwai wanda ya fi cancanta da aikin to hakika ya kha’inci All..da manzonsa da kuma muminai (s).

A wani hadisin, ya na cewa: All..ya na kudaitarwa, sosai kan, wajen zaben mafi korewar mutane,  wanda ya kasance mafi cancanta ga wani matsayi. Lalle, su sanya maslahar al-umma ne abin lura a wajen su, a lokacin zaben. Su kasance amintattu a cikin abinda suke karba daga hannun mutane.

Sannan su zamanto amintattu a kashe kudaden kan abubuwan jin dadin rayuwar mutane. Sannan su tafiyar da al-amuran mutanen a cikin adalci kadai.   

Wannan ka da ya kasance, da yawan shekaru ne ake zabe ba, sai dai ya kasance tare da kwarewa da kuma sanin makamar aiki, da sanin abubuwan da mutane suke bukata.

Don haka manzon All..(s) a cikin shugabantar da Usama Dan Zaidu ya kakkabo wasu daga cikin wadanda suke takara da Amirulmuminina (a) kan shugabancin al-ummar musulmi a bayansa.

Ya karya zukatansu, daga neman wannan mukamin, ya kuma kashe guiwarsu da yunkurinsu na neman wannan matsayin. Ya nisantar da su nesa ba kusa ba daga wannan burin nasu.

Sannan su ma sun fahinci hakan, daga wajen manzon All…(s).  Baku ga cewa, Umar ya na cewa: Ya kai Usaman! Manzon All.. zai yi wafati kana shugabana?

 Basu gushe ba suna jan kafa, sun ci ga ba da sabawa umurnin manzon All..(s) har sai da ya yi wafata. (s).

Wannan kadan Kenan na abinda za’a iya fahinta, na shugabatar da Usama dan shekara kimani 17 kan shaihunan kurasihawa, da kuma wasu shuwagabannin ansar wadanda suka kodayin shugabancin al-ummar musulmi bayan wafatin manzon All.. (s).

Har’ila yau wannan ya tabbatar mana akwai makirci babba da aka kulla don hana Imam Ali (s) za ma a kan kujerar da shi kadai ya dace da ita bayan manzon All..(s).

Daga nan sai zazzabi ta yi tsanani wa manzon All..(s), a lokacin, matansa suna kusa da shi, a duk lokacinda suka sa hannunsu a kansa suna jin yadda yake zafi.

Sukan sanya ruyuwan sanyi kusa da shi, a duk sanna ya sa hannunsa cikinsa sai ya shafa fuskansa da sanyin hannunsa..

Sai mutane su na ta kai kawo suna bankwana da shi, sai da suka taru a gidansa,  sai ya fada masu:

Yace: Ya ku mutane, an kusa a dauki raina, daukewa mai sauki, sannan a tafi da ni. Hakikin na gabatar da maganganu, don sauke uzuri da ke kaina a kanku. Sai dai lalle ni ina barin Littafin All..mai girma da daukaka da kuma zurriya ta  Ahlubaiti na.  Sai ya kama hannun Aliyu(a) ya daga ta, ya ce: Ga Aliyu nan tare da Alkur’ani , kuma kur’ani ya na tare da Ali ba za su rabu ba, har sai sun riskeni a tabki.

Abinda yakamata al-umma ta yi shi ne ta bi umurnin manzon All..ta bi abinda ya fada mata ta bi Amirulmuminina (s), ta mika masa shugabanci, don shi ne kawai zai tafiyar da al-amarinsu kan koyarwar Alkur’ani mai girma. Da kuma hukunci da hukuncin All..T

Ta yin haka ne kawai za ta tsira daga dukkan tawaya, kuma fitinu ba za su same ta ba, haka ma dukkan hatsurra ba za su sameta ba.

Daa kuwa musulunci, zai dau matasyinsa kai tsaye, a duniya, ya kuma sami iko da da ita gaba daya. Ya cika shi da adalci.

Har’ila yau kafin rasuwarsa manzon All..(s) ya daura rawaninsa, sai ya je masallaci ya hau mimbarinsa, sai ya ce masu, Lalle Ubangijina ya hukunta, ya kuma rantse kan cewa ba zai yafe zuluncin azzalumi ba, don haka ina hadaku da All…duk wani mutum wanda yake da wani abu da na yi masa sai ya tashi ya fada don yayi kisasi, saboda kisasi a gidan duniya yafi mani da kisasa a Lahira. Inda za’a yi hakan a gaban mala’iku da annabawa…}.

Manzon All..(s) ya na nuna masu kan cewa zalunci ko wace irice, mutum ya warware shi a lduniya ya fi masa a yi masa adalci a lahira.

An dade ba wanda yayi Magana sai wani mutum daga karshen masallacin, mai suna Sawadat dan Qais, sai ya ce: ee ya manzon All..(s) ka taba doka na a wani lokaci a ciki na. don haka ina son kisassi.

Sai manzon All..(s) yace masa ya zo . sannan ya aiki Bilal ya kawo bulala daga gidansa, da ya kawo sai mutane suna gani me mutumin nan za iyi yi wa manzon All..(s) a cikin wannan halin da yake na rashin rafiya.

Sai Sawada ya zo kusa yana karkarwa., saboda haibar manzon All.. sai ya ce: Ya manzon All..ka kwaye mani cikinka, sai ya ce ya manzon All..(s) kayi mani izini in Sanya bakina a kan cikinka?, sai yace masa ee. Sai ya Sanya bakinsa a kan cikin manzon  All… idanunsa ya na zubar da hawaye.

Sai ya na cewa  ina neman tsari daga wuta albarkan wurin kisasi da ga manzon All..(s), a ranar lahira.

Sai manzon All..(s) ya ce masa, za ka yi kissasi ne ko kai yi afwa?, sai yace,  sai yace Afwa ya manzon All..(s). 

Sai manzon All..(s) ya daga hannayensa ma su albarka ya na uddu’a yana cewa: Ya Ubangiji! ka gafartawa Sawadah, saboda afwar da ya yi wa annabinka Muhammadu. (s).

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: manya manyan sahabban ya manzon All Ya manzon All

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnati Za Ta Haramta Amfani Da Tankoki Masu Ɗaukar Lita 60,000 Aiki Daga Maris 1

Gwamnati Za Ta Haramta Amfani Da Tankoki Masu Ɗaukar Lita 60,000 Aiki Daga Maris 1

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sadaukantaka, Kunya Da Kawar Da Kai Na Annabi Muhammadu (SAW)
  • Iran Ta Yi Tir Da Shugaban Hukumar IAEA Saboda Sanya Siyasa Da Daukan Bangare A Jawansa Na Baya Bayan Nan
  • Tashar Jiragen Sama Ta Rafikul Hariri Int. Na Birnin Beirut Yana Ciki Da Masu Shiga Kasar Saboda Jana’izar Shaheed Nasarallah
  • Gwamnati Za Ta Haramta Amfani Da Tankoki Masu Ɗaukar Lita 60,000 Aiki Daga Maris 1
  • Amurka Ba Ta Sauya Ba Ko Kadan
  • Rayuka 10 da dukiyar N11bn sun salwanta yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a Kano
  • Hamas: Za A Mika Gawawwakin ‘Yan Mamaya Da Kuma Fursunoni Rayayyu A Ranakun Alhamis Da Asabar
  • Kissoshin Rayuwa. Sirar Imam Alhassan (a) 19
  • DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi
  • Jaridar Maariv Ta Isra’ila Ta Bayyana Wasu Daga Cikin Hasarorin Da Yakin Gaza Ya Janyo Wa Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya