Shugaba Tinubu Zai Ziyarci Takwaransa Na Faransa Emmanuel Macron
Published: 5th, February 2025 GMT
A yau ne shugaba Bola Ahmed Tinubu zai tashi daga Abuja zuwa birnin Paris na kasar Faransa a wata ziyarar kashu kai, inda daga nan zai wuce Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.
A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ya ce a birnin Addis Ababa, shugaba Tinubu zai bi sahun shugabannin Afirka a zaman taron majalisar zartarwa karo na 46 da kuma zaman taro na 38 na shugabannin kasashen kungiyar tarayyar kasashen Afirka wato AU, wanda aka shirya daga ranar 12 zuwa 16 ga watan Fabarairun 2025.
Shugaban zai isa Addis Ababa a farkon mako mai zuwa don halartar taron kungiyar ta AU.
Yayin da yake kasar Faransa, shugaba Tinubu zai gana da takwaransa na Faransa, shugaba Emmanuel Macron.
Bello Wakili
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Faransa Taron AU Ziyara
এছাড়াও পড়ুন:
Ruwa Ya Ci Rayukan Mata Biyu A Kano
Mazauna karamar hukumar Gezawa ta Kano sun shiga cikin tashin hankali da makoki sakamakon nutsewar wasu mata biyu a cikin wani tafki.
Rahotanni sun nuna cewa matan (an sakaya sunansu) sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke wanka a kogi bayan sun dawo daga aiki a wata masana’antar sarrafa hibiscus.
A cewar jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano Saminu Yusif Abdullahi Gezawa hukumar kashe gobara ta samu kiran gaggawa daga ‘yan banga da ke yankin tare da bayyana cewa “Yan uwan matan biyu ne suka kai rahoton lamarin ga dan banga”
Ya yi nuni da cewa, nan take aka tura tawagar masu aikin ceto zuwa wurin, inda suka yi nasarar zakulo gawarwakin su a sume, daga bisani jami’an lafiya suka tabbatar da mutuwarsu.
Saminu ya bayyana cewa an mika gawarwakin ga wani dan sanda Musa Garba na sashin ‘yan sanda na Gezawa.
Ya shawarci jama’a da su daina zuwa kusa da kogi domin gujewa abubuwan da ba a zata ba.
KHADIJAH ALIYU