Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Yabawa Gwamna Namadi Bisa Amincewa Da Tsarin Bada Tallafi A Mazabu
Published: 5th, February 2025 GMT
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta yabawa Gwamna Umar Namadi bisa amincewarsa ga manufar majalisar, ta bullo da tsarin bada tallafin sana’oi na mazabu ba tare da jinkiri ba.
Shugaban Majalisar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya bayyana haka a lokacin da yake kaddamar da rabon tallafi wanda wakilin mazabar Kanya a majalisar dokokin jihar,Alhaji Ibrahim Hashim Kanya, ya bai wa al’ummar garin Kanya dake karamar hukumar Babura.
Yana mai cewar, majalisar ta bullo da tsarin bada tallafin domin mara baya ga Kudurorin Gwamna Umar Namadi guda goma sha biyu, ta fuskar bunkasa tattali da samar da ayyukan yi ga jama’a.
A jawabinsa, wakilin mazabar Kanya Alhaji Ibrahim Hashim Kanya, ya ce mutane 1,350 ne za su amfana da tallafin daga mazabu biyar.
Ya kuma yi kira ga wadanda su ka rabauta da su yi cikakken amfani da tallafin domin su zamo masu dogaro da kawunansu.
A jawabinsa na maraba, Shugaban karamar hukumar Babura, Malam Hamisu Muhammad Garu, ya bayyana kudurinsa na aiki tare da bangaren majalisa domin ciyar da yankin gaba.
Kazalika, ya yi addu’a ga Allah SWT ya albarkaci abin da aka rabawa jama’a a yankin na Kanya.
Wakilinmu ya bamu rahoton cewar, taron ya samu halartar wasu daga cikin ‘Yan majalisa da Hakimin Kanya da kwamishinan ciniki da dai sauransu.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa Majalisar Dokoki
এছাড়াও পড়ুন:
Zulum Ya Gana Da Yaron Da Aka Ci Zarafi, Ya Ba Shi Gida, Tallafin Karatu
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp