Aminiya:
2025-03-23@23:07:29 GMT

Gobara ta yi ajalin almajirai 17 a Zamfara

Published: 5th, February 2025 GMT

Wata gobara da ta tashi a wata makarantar tsangaya da ke Ƙaramar Hukumar Kaura-Namoda a Jihar Zamfara, ta yi ajalin almajirai 17.

Dukkanin almajiran sun ƙone ƙurmus, ta yadda ba a gane kowa a cikinsu ba.

Saura ƙiris Bello Turji ya zo hannu – Ministan Tsaro Tinubu ya ƙara kasafin kuɗin 2025 zuwa N54.2trn

Shaidu sun bayyana cewa gobarar ta farq ne cikin daren ranar Talata, kuma ta ɗauki kimanin sa’o’i uku tana ci.

Rahotanni sun bayyana cewar wasu almajirai 16 sun samu munanan raunuka a gobarar.

Wani mazaunin yankin, Abdulrasaq Bello Kaura, ya bayyana cewa gobarar ta fara ne sakamakon kamawar wasu itatuwa da aka ajiye.

Wani ganau ya shaida cewar, “Abin ya faru ne a makarantar Malam Ghali, a cikin ɗakin karatu.

“Akwai kusan almajirai kusan 100 a cikin gidan. Bayan da aka fitar da su, sai aka ɗauka babu kowa a ciki.

“Amma bayan gobarar ta lafa, sai aka dawo aka ga sassan jikin wasu kamar ƙafafu, hannaye, da kuma gawarwakin waɗanda suka rasu bayan sun ƙone ƙurmus.”

An yi jana’izar waɗanda suka rasu a ranar Laraba.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Kaura-Namoda, Kwamared Mannir Muazu Haidara, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce yana kan hanyarsa ta zuwa wajen da lamarin ya faru domin samun ƙarin bayani.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Almajirai Gobara Makarantar Tsangaya Zamfara

এছাড়াও পড়ুন:

Bam ya kashe mutum 4 da jikkata wasu a Borno

Aƙalla fasinjoji huɗu ne suka mutu yayin da wasu huɗu suka jikkata sakamakon fashewar wani bam a ƙarƙashin wata motar kasuwanci a ƙaramar hukumar Biu ta Jihar Borno.

Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta tabbatar ta afkuwar lamarin.

Gobara ta kashe ɗan shekara 7 a sansanin ’yan gudun hijira ’Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in FRSC a Benuwe

Majiyoyin leƙen asiri sun shaidawa Zagazola Makama cewa, lamarin ya faru ne a ranar 19 ga Maris, 2025, da misalin ƙarfe 2:30 na rana a lokacin da wata mota ƙirar Golf 3 ta Wakil Fari ta tashi daga garin Kimba zuwa garin Biu.

Bayan sun isa mahaɗar Sabon Garin Kimba, motar ta taka wata nakiya (IED), wanda ya kai ga fashewa da ta kashe fasinjoji mata uku da fasinja namiji guda nan take.

Majiyar na cewar wasu fasinjoji hudu kuma sun sami raunuka daban-dabam kuma nan da nan an kai su babban asibitin Biu don yi musu jinya.

Daga bisani likitoci sun tabbatar da mutuwar wadancan mutane huɗu sannan aka ajiye su a ɗakin ajiyar gawa na asibitin kafin a miƙa su ga ’yan uwansu don yi musu jana’iza.

Bincike na farko ya nuna cewa ’yan ta’addar ISWAP ne suka dasa waɗannan bama-bamai (IEDs) a tunanin sojoji za su taka.

Jami’an soji sun tabbatar da faruwar hakan, tare da duba ƙarin barazanar da ake fuskanta daga wadannan ‘yan ta’addan don tabbatar da tsaro ga masu amfani da hanya.

Hukumomi sun kuma ƙaddamar da gangamin wayar da kan al’umma kan haɗarin bama-bamai da ba su fashe ba, don kaucewa faruwar lamari irin ya hakan.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gobara ta tashi a gidan mai sakamakon fashewar tanka a Neja
  • ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 10, sun jikkata 14 a Zamfara
  • An Kashe Askarawa 6 da ‘Yan Sa-kai 4 A Zamfara 
  • Bam ya kashe mutum 4 da jikkata wasu a Borno
  • Gobara ta kashe ɗan shekara 7 a sansanin ’yan gudun hijira
  • Sallah: Tinubu Ya Raba Wa ’Yan APC Buhun Shinkafa 7,000 A Zamfara
  • Gobara Ta Kashe Yaro A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira A Maiduguri
  • Nasiru Ahali Shahararren masanin masana’antu a Kano ya rasu
  • Gwamnatin Yobe na ciyar da almajirai a Tsangayu 85 kullum
  • Araghchi : Iran za ta mayar da amsa ga wasikar Trump cikin kwanaki masu zuwa