Kasar Iran Ta Bayyana Shirinta Na Mayar Da Martani Ga Duk Wata Barazana Kanta
Published: 5th, February 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran za ta mayar da martani ga duk wata barazana ko matsin lamba gwargwadon tsayin dakarta
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Iran ta sha tabbatar da cewa a shirye take ta gudanar da huldar siyasa da diflomasiyya don tabbatar da moriyar kasa, kuma tana shirye ta gudanar da kumajin siyasa da diflomasiyya wajen kare muradunta da tsaron kasa, sannan tana da azamar daukan duk wani matakin kare kanta da masalaharta tare da mayar da martani ga duk wata barazana ko matsin lamba gwargwadon tsayin daka da gwagwarmayarta.
Isma’il Baqa’i ya bayyana haka ne a yayin da yake mayar da martani ga tambayar cewa; Maganganun da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi a baya-bayan nan dangane da Iran, inda ya jaddada cewa: Zarge-zargen da ake yi kan Iran cewa tana yunkurin kera makaman kare dangi, kawai da’awar karya ce tsagwaranta. Sannan Iran din ta tabbatar da karce-karyacensu sau da dama, kuma duk wanda ya nemi tabbas kan wannan lamari zai iya samun cikin sauki.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasashen Larabawa Na Yankin Tekun Farisa Sun Yi Fatan Al-Khairi Ga Iran Da Amurka A Tattaunawar Shirin Nukliyar Kasar
Babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa na yankin tekun Farisa (PGCC) ya yi fatan alkhairi ga kasashen Iran da Amurka a tattaunawa ba kai tsaye ba a tsakaninsu dangane da shirin Nukliya ta kasar Iran na zaman lafiya wanda suka fara, a birnin Mascat na kasar Omman a ranar Asabar da ta gabata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jasem Mohamed AlBudaiw yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa, kungiyar tana bukatar gidan an warware matsaloli tsakanin kasashen duniya ta hanyar tattanawa. Haka ma tsakanin kasashen yankin.
AlBudaiw ya yabawa kasar Omman da shirya wannan tattaunawar, sannan ya yi fatan tattaunawan da aka fara zai kai ga rage tada jijiyoyin wuya a yankin da kuma kasashen duniya, ya kuma ce kasashen yankin suna fatan zasu kai ga sakamako mai kyau tsakanin kasashen biyu.
Gwamnatin kasar Iran dai tana har yanzun suna shakkar kasar Amurka saboda yawan yaudarar da tayiwa kasar a baya. Musamman fitar kasar daga yarjeniyar JCPOA a shekara ta 2018. Da kuma yawan takunkuman da ta dorawa a kasar tun lokacin.
Daga karshe babban sakataren kungiyar ta PGCC ya ce tana fatan za’a kawo karshen duk wani rikici a gabas ta tsakiya daga ciki har da na HKI a falasdinawa a Gaza ta hanyar tattaunawa da fahintar Juna.