Ɗan sanda ya harbe kansa har lahira a Nasarawa
Published: 5th, February 2025 GMT
Wani Jami’in Ɗan Sanda da ke aiki a ofishin ’yan sanda na yankin Mada a Jihar Nasarawa, ya harbe kansa da bindiga har lahira.
An gano ɗan sandan, mai suna Dogara Akolo-Moses, yana aiki ne a Ƙaramar Hukumar Nasarawa Eggon lokacin da ya kawo ƙarshen rayuwarsa.
’Yan sanda sun kama baƙin haure 165 a Kebbi Sarkin Jiwa a Abuja ya yi rashin mahaifiyaShaidu sun bayyana cewar ya shiga wani ɗaki sannan ya harbe kansa da bindiga.
Sautin harbin bindigar ne ya jawo hankalin abokan aikinsa, waɗanda suka garzaya zuwa ɗakin, inda suka same shi kwance cikin jini da bindiga a gefensa.
Har yanzu ba a san dalilin da ya sa ya hallaka kansa ba.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa, Ramhan Nansel, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce rundunar tana gudanar da bincike don gano abin da ya sa jami’in ya ɗauki wannan mummunan mataki.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Wasu manyan ’yan Nijeriya sun yi wa Gwamna Radda ta’aziyya a Saudiyya
Wasu manyan ’yan Nijeriya da suka tafi Umarah sun yi wa Gwamnan Katsina Dikko Umar Radda ta’aziyya a Saudiyya.
A safiyar Lahadi ce dai Allah Ya karɓi rayuwar mahaifiyar Gwamnan, Hajiya Safara’u Umaru Baribari bayan shafe tsawon lokaci tana jinya a Jihar Katsina.
Wata mata ta haifi jaririn da ba nata ba NAJERIYA A YAU: Yadda watan Ramadana ke tasiri a harkokin kasuwanciBayan rasuwar ce gwamnoni da wasu fitattun ’yan siyasa da a halin yanzu suna ƙasa mai tsarki suka kai wa Gwamna Radda ziyara domin jajanta masa dangane da wannan babban rashi.
Daga cikin gwamnonin akwai Mohammed Umar Bago na Jihar Neja, da Farfesa Babagana Zulum na Jihar Borno da Gwamna Uba Sani na Kaduna, da Dauda Lawal Dare na Zamfara da kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe
Sauran fitattun ’yan siyasar da suka ziyarci Gwamna Radda sun haɗa da Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, da tsohon Gwamnan Bauchi, Ahmed Mu’azu.
Akwai kuma fitaccen attajirin nan kuma ɗan kasuwa, Alhaji Dahiru Mangal da kuma tauraron tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya ta Super Eagles, Ahmed Musa da su ma suka jajanta wa gwamnan a kan rashin.
Dukkansu sun bayyana alhini tare da roƙon Allah Ya jiƙan Hajiya Safara’u Ya sa ta huta.