Shugabannan Palasdinawa daga cikin har da kungiyar Hamas da Jahadul Islami duk sun ki amincewa da shirin trump na sake kwace Gaza, kafin haka kuma shugaban ya ce dole Falasdinawa su daga yankin kafin ya kwace shi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran  ya nakalto shuwagabannin Palasdinawan suna allawadai da shugaban, sun kuma kara da  cewa abinda HKI bata samu da yakin wattnin 15 ba, shugaba Trump ya na ya ba su da sauki da kuma wayon da za’a yiwa yaro.

A ranar talata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa zai kwace Gaza a hannun Palasdinawa sannan ya sake gina shi.

Falasdinawa kimani 61,700 suka rasa rayukansu a yayin da fiye da 100,000 ji rauni a yakin watanni 15 da suka fafata da HKI a Gza..

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Jama’ar Gabon sun kada kuri’a a zaben shugaban kasa, na farko bayan mulkin zuri’ar Bongo

A Gabon, yau Asabar ne Jama’ar kasar suka kada kuri’a  domin zaben shugaban kasar, a karon farko bayan kifar da iyalan gidan Bongo daga mulkin kasar.

Janar Brice Oligui Nguema, wanda ya kifar da mulkin Ali Bongo na daga cikin ‘yan takarar dake fafatawa a zaben daga cikin ‘yan takara guda takwas.

Sauran yan takarar sun hada da Firaministan kasar Alain Claude Bilie-by-Nze, wanda ya rike wannan mukami a lokacin mulkin Bongo, da kuma wasu manyan kusoshin tsohuwar jam’iyya mai mulki ta PDG.

Kimanin mutum miliyan daya ne aka tantance su kada kuri’a a zaben, daga cikin jimilar miliyan biyu da rabi na kasar.

A karfe 06:00 na yamma agogon kasar wato 05:00 na yamma agogon GMT, na yau aka tsara rufe rumfunan zaben.

Za a iya fara sanar da sakamakon zaben daga gobe Lahadi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Kasar Iran Ya Mika Ta’aziyyar Ta Rasuwar Wanda Ya Assasa Hukumar  Makamashin Nukiliya Ta Iran
  •  Tsoffin Ma’aikatan Hukumar Leken Asiri HKI  Mosad Sun Shiga Cikin Masu Kiran A Kawo Karshen Yaki Da Gaza
  • Sojojin Yemen Sun Kakkabo Jirgin Yakin Amurka Wanda Ake Sarrafa Shi Daga Nesa Na 19
  • Hukumar OCHA Ta Bayyana Cewa Yahudawan Sahyoniyya Sun Ninninka Ayyukan Korar Falasdinawa A Yamma Da Kogin Jordan
  • Brice Ologui Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Gaban Da Kashi 90.35% A Jiya Lahadi
  • Al’ummar Mauritaniya Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Nuna Adawa Da Yakin Gaza
  • Dagewa Iran Takunkuman Zalunci Na Daga Cikin Manufofin Tattaunawa Da Amurka: Aref
  • Ukraine na Fuskantar Wata Barazana, Dangane Da Bukatar Amurka Na Kwace Iko Da Cibiyar Gas Na Rasha  A cikin Kasar
  • Jiragen Yakin Kasar Amurka Suna Rusa Cibiyoyin Ilmi A Hare-Haren Da Suke Kaiwa Kasar Yemen
  • Jama’ar Gabon sun kada kuri’a a zaben shugaban kasa, na farko bayan mulkin zuri’ar Bongo