Kwamishinan ‘Yansandan Kano Ya Gana Da Masu Ruwa Da Tsaki Kan Inshorar Motoci
Published: 6th, February 2025 GMT
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya gana da masu ruwa da tsaki a harkokin sufuri domin tattauna yadda ake ci gaba da aiwatar da aikin inshorar motoci na wasu motocin da ke bin hanyoyin jihar Kano.
Taron wanda ya samu halartar shuwagabannin kungiyar ma’aikatan sufuri ta kasa (NURTW), kungiyar masu safara a tituna ta Najeriya (NARTO), kungiyar ma’aikatan sufurin mota ta kasa (RTEAN), da kuma shugaban tashar motocin Kano Line da nufin tabbatar da bin ka’idojin inshora.
CP Dogo ya yabawa masu ruwa da tsaki bisa hadin kan da suka bayar, inda ya ce sama da kashi 85% na masu ababen hawa sun mallaki takardar inshorar motocin da ake bukata daga ranar farko da aka fara aiwatar da su.
Ya kuma ja hankalin jama’a da su ci gaba da bin ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa, inda ya jaddada muhimmancin kiyaye hanya.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano za ta ci gaba da aiwatar da ka’idojin inshorar motoci na wasu kamfanoni, bisa ga umarnin babban sufeton ‘yan sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun. CP Dogo ya bukaci masu ruwa da tsaki da su wayar da kan ‘yan kungiyar su hada kai da ‘yan sanda tare da kai rahoton duk wani abu da ake zargi.
Jama’a na iya kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko ta hanyar tuntuɓar masu zuwa: 08032419754, 08123821575, ko 09019292926.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO/Wababe
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Inshara
এছাড়াও পড়ুন:
CMG Ya Kaddamar Da Nuna Fina-Finai Da Shirye-Shiryen Talabijin Na Kasar Sin Masu Inganci A Malaysia
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp