An kashe wa ma’aurata ’ya’yansu uku a boye gawarsu a firinji
Published: 6th, February 2025 GMT
Wasu ma’aurata sun tsinci gawarwakin kananan ’ya’yansu uku a boye a cikin wani firinji a yankin Nnewichi da ke Nnewi a Jihar Anambra.
Iyayen yaran, Mista Udochukwu da Misis Chikazor Ejezie, sun tsinci gawar ’ya’yan nasu a cikin firinji ne bayan da suka dawo gida daga wurin aiki.
Bayan dawowarsu ne suka samu gidan a bude ba yadda suka saba ba, kasancewar yaran suka kulle gidan a duk lokacin da za su je wasa.
Da shigarma’auratan cikin gidan ne kuma suka ga gawarwakin yaran an sanya a cikin firinjin kayan kankara.
Zargin Tinubu: Gaskiya Naja’atu ta fada kan Nuhu Ribadu —El-Rufai NAJERIYA A YAU: Tasirin Yankan Angurya A Rayuwar Mata Kotu ta ɗaure Farfesa shekara 3 kan aikata maguɗin zaɓeLamarin da ya faru a karshen mako ya tayar da kura, musamman a kafofin sada zumunta.
Bayan hakan ne gwamnatin jihar ta yi alkawarin bin diddigi tare da kama masu hannu a wannan aika-aika.
A yayin ziyarar da ta kai wurin, Kwamishinar Harkokin Mata da Walwalar Jama’a, Misis Ify Obinabo, ta ba da tabbacin yin duk mai yiwuwa wajen ganin an yi wa yaran adalci.
Kwamishinar, ta kuma jaddada haka a lokacin da ta ziyarci Asibitin Koyarwa na Jami’ar Nnamdi Azikiwe da ke Nnewi, inda aka ajiye gawarwakin yaran.
Mazauna unguwar sun bayyana lamarin a matsayin babban tashin hankali a yayin da suke ta tausaya wa ma’auratan.
Tuni dai hukumomin jihar Anambra suka kaddamar da bincike kan lamarin da nufi lalubo bakin zaren.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Anambra kananan yara yara
এছাড়াও পড়ুন:
Za’a Gudanar Taron Tattaunawa Tsakanin Rasha Ta Amurka A Karo Na Biyu 2 A Birnin Rayad na Kasar Saudiya
A gobe Litinin 24 ga watan Maris ne tawagogin masu tattaunawa na kasashen Amurka da Rasha zasu hadu a birnin Rayida na kasar Saudiya don ci gaba da tattaunawan da suka fara a yan makonnin da suka gabata dangane da yakin da ke faruwa a Ukraine, shekaru fiye da 3 da suka gabata, da kuma dangantaka a tsakanin kasashen biyu.
Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto Yury Ushakov mai bawa shugaba Putin shawara kan al-amurin siyasa yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa Sanata Georgy Karasin ne zai jagoranci tawagar masu tattaunawa ta kasar Rasha sannan ta kasar Amurka an rika an samar da tawagar, wasu zata hadu da na Rasga a gobe litin a birnin Riyad.
Kafin haka dai shugaban kasar Rasha Vladimir Putin sun tattauna da tokwaransa na kasar Amurka Donal Trump kan al-amura da dama wadanda suka shafi yakin a Ukraine da tsagaita budewa juna wuta na wata guda da kuma wasu al-amura.
Karsin daga karshe ya ce yana fatan tattaunawan zata yi armashi.