Ɗan firamare ya je makaranta da bindiga yana barazanar harbe ɗalibai
Published: 6th, February 2025 GMT
An kama wani ɗalibin firamare mai shekara 13 ɗauke da bindiga a makaranta, inda yake barazanar harbe abokan karatunsa da ita.
Bayan nan ne jami’an tsaro suka yi nasarar kama shi a Makarantar Firamare ta St. Paul da ke ƙauyen Ikot Ibiok a Ƙaramar Hukumar Eket a Jihar Akwa Ibom.
A safiyar Alhamis ne kakakin runduanr ’yan sandan jihar, DSP Timfon John, ta sanar da kama yaron.
DSP Timfon John ta bayyana cewa, a yayin bincike sun gano cewa yaron ya shafe kimanin wata uku yana zuwa da bindigar makaranta.
An kashe wa ma’aurata ’ya’yansu uku an ɓoye gawarsu a firinji Zargin Tinubu: Gaskiya Naja’atu ta fada kan Nuhu Ribadu —El-Rufai NAJERIYA A YAU: Tasirin Yankan Angurya A Rayuwar MataTa bayyana cewa ya shaida musu cewa tun a watan Nuwambar shekarar 2024 ya ɗauko bindigar daga kwabar tufafi da ke ɗakin mahaifinsa yake amfani da ita.
Ta ce bayan samun rahoto ne, “ba tare da ɓata lokaci ba rundunar ta garzaya ta kama yaron tare da ƙwace bindigar hannun, wadda ƙirar gida ce.
“A yayin bincike yaron ya shaida mana cewa tun watan Nuwambar 2024 bindigar take hannunsa, kuna ya dauko ta ne daga kwabar mahaifinsa, wanda shi ma daga bisani muka kama shi, muna bincikar su tare.”
Ɗan shekara 60 ya lalata ’yar shekara 9Ta ce rundunar ta kuma cika hannu da wani ɗan shekara 60 da ya yi wata yarinya mai shekara tara a duniya fyade.
Ta ce dubun tsohon ta cika ne bayan mahaifiyar yarinyar ta kai ƙara a ofishin ’yan sanda daga ƙauyen Afaha Offiong, da ke yankin Nsit Ibom.
Jami’ar ta bayyana wa ’yan sanda cewa bayan ta aiki ’yar tata ne tsohon ya tare ta ya shigar da ita cikin jeji ya keta matuncinta, inda daga baya ya ba ta Naira 200.
Daga bisani jami’an rundunar suka je suka cika hannu da shi kuma nan gaba za a gurfanar da shi a gaban kotu domin ya girbi abin da ya shuka.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in FRSC a Benuwe
Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wani jami’in Hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) Nathaniel Terwanger Kumashe a ƙauyensa da ke ƙaramar hukumar Tarka a Jihar Benuwe.
An samu rahoton cewa wanda aka yi garkuwan ya taso ne daga Makurdi sansaninsa, domin halartar jana’izar ɗan uwansa da ya rasu a lokacin da aka ɗauke shi zuwa wani wuri da ba a san inda yake ba.
Nasiru Ahali Shahararren masanin masana’antu a Kano ya rasu Kotun ƙoli ta tabbatar da Anyanwu a matsayin sakataren PDPWani kawun wanda aka yi garkuwan, tsohon mai baiwa gwamnan Jihar Benuwe shawara kan harkokin sufuri, Cif Yimam Aboh, ya shaidawa manema labarai a Makurdi ta wayar tarho cewa an ɗauke jami’in, Insfekta Kumashe a daren Laraba da misalin ƙarfe 10 na dare.
Ya ce, ’yan bindigar sun yi ta harbi don tsoratar da ’yan uwa da maƙwabta kafin su yi awon gaba da wanda suka yi garkuwan daga gidansu da ke Tse Aboh, Uchi-Mbakor a ƙaramar hukumar Tarka.
Ya kuma bayyana cewa, Kumashe ya koma gidansa ne bayan rasuwar ɗan uwansa wanda za a yi jana’izarsa a yau lokacin da masu garkuwar suka farwa gidan.
A halin da ake ciki, jami’ar hulɗa da jama’a ta Hukumar FRSC a Benuwe, Ngozi Ahula, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ƙara da cewa an kai rahoton lamarin ga ’yan sanda.