Daliban Kasar Bangaladesh Sun Kona Gidan Tsohon Shugaban Kasa
Published: 6th, February 2025 GMT
Rahotanni da suke fitowa daga kasar ta Bangaladesh sun ce, a jiya Laraba da marece ne wasu dalibai da sauran mutanen gari sun ka cinna wuta a cikin gidaje masu yawa, da su ka hada da na tsohon shugaban kasa Mujibur Rahman. Abinda yake faruwa yana nuni ne da dambaruwar siyasa da kasar take ci gaba da fuskanta da kuma rashin gamsuwar da mutanen kasar nunawa akan halin da ake ciki.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Iran Ya Tattauna Da Sarkin Kasar Qatar Kan Muhimmancin Hadin Gwiwa Da Taimakekkeniya Tsakaninsu
Shugaban kasar Iran da Sarkin kasar Qatar sun jaddada muhimmancin hadin gwiwa da taimakekkeniya tsakanin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian da sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamid Al Thani sun gudanar da taron manema labarai na hadin gwiwa a birnin Tehran, inda suka jaddada karfin dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da kuma muhimmancin kara inganta taimakekkeniya a tsakanin kasashensu.
Shugaban na Iran ya fada a yammacin yau Laraba cewa: Ci gaba da tarukan tsakanin jami’an kasashen biyu ke yi na tabbatar da kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu, yana mai jaddada karfafa alaka da kasashe makwabta, musamman kasar Qatar, a matsayin wani muhimmin ka’ida na manufofin ketare na Iran.
Shugaban kasar ya ci gaba da cewa: Sun tattauna da Sarkin Qatar kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu ta hanyar da za ta tabbatar da moriyar kasashensu, kuma an yanke wasu muhimman shawarwari na raya kasa da zurfafa dangantaka da bude sabbin hanyoyin hadin gwiwa. Sarkin Qatar ya kuma jaddada bukatar samar da sabbin damar gudanar da hadin gwiwa.
Shugaba Pezeshkian ya kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi imanin cewa, kasashen yankin suna da karfin daukar matakai na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin, bisa tushen kyakkyawar makwabtaka da mutunta juna da kyautata mu’amala mai ma’ana, da share fagen kafa wani tsari na hadin gwiwa da taimakekkeniya.